Home / News / MUNA KIRA GA DAUKACIN YAN TAKARAR SHUGABAN KASA SU MARAWA TINUBU BAYA – KAILA MUHAMMADNI

MUNA KIRA GA DAUKACIN YAN TAKARAR SHUGABAN KASA SU MARAWA TINUBU BAYA – KAILA MUHAMMADNI

 

AN yi kira ga daukacin masu takarar shugaban kasa da su ajiye dukkan bukatarsu domin marawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya ta yadda Najeriya za ta ci gaba.

A batun satar mai an fara yin sa ne a shekarar 1983, tun daga wannan lokacin sai satar mai ta zama kamar wani abun kwarai saboda akwai mutane da yawa da suka shiga cikin batun satar nan.

“Akwai yan siyasa,wasu jami’an tsaro da sauran wasu mutane da yawa da wasu ma kawai suna kwance a cikin wuraren da suke kawai su rika ganin makudan biliyoyi na zuwa masu haka kawai, wanda hakan ba dai- dai bane ga rayuwar kasa tare da jama’arta.

“Saboda haka muna kara ankarar da yan Najeriya da su tashi tsaye wajen ganin sun taimakawa kasar su, musamman su yi maganin wadannan masu satar mai da ake kiyasta cewa ba su kai mutane Dubu ba, amma suna wahalar da dimbin jama’a.

“Tasirin wannan samun mai a Arewa na da matukar amfani kwarai, kuma muna godiya ga shugabannin Arewa na da can irin su Sardauna, Tafawa Balewa da sauransu da suka ajiyewa Arewa man da take da shi da dadewa har ga shi a yanzu an fara tono mai a arewacin Najeriya.

“Kamar yadda dan takarar shugaban kasa Bola Tinibu ya fadi cewa za a ci gaba da aikin tonon mai da isakar Gas da sauran ma’adanan da ake da shi a Arewa, sabanin irin yadda wasu suka ce Sayarwa za su yi kawai”.

 

Muna kira ga yan majalisar dokokin tarayyar Najeriya da su tabbatar sun kama wadannan masu satar mai ko a ina suke domin ba su fi karfin doka ba, saboda sun dade suna wasa da rayukan jama’a da dama sakamakon son zuciyar da suke fama da shi na sace man Najeriya.

About andiya

Check Also

Kaduna: LP Guber Candidate, Asake, Meets Muslim Clerics, Assures Of Fairness To All

The Labour Party, LP, governorship candidate in Kaduna State, Hon. Jonathan Asake, has assured the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.