Home / Labarai / Muna Neman A Bude Layukan Waya – Tambuwal

Muna Neman A Bude Layukan Waya – Tambuwal

 

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa sun rubutawa ma’aikatar kula da harkokin Sadarwa ta kasa da ta bude masu layukan wayar salula da can kwanan baya aka rufe domin jami’an tsaro su samu sukunin aiwatar da ayyukansu na yaki da yan bindiga.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da muka samu daga gidan Gwamnatin Jihar Sakkwato da ke bayanin cewa a halin yanzu tuni Gwamnatin ta rubutawa Ma’aikatar sadarwa domin neman bukatar a bude layukan wayar sadarwa saboda jami’an tsaro su samu sukunin gudanar da aikin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a.
Indai za a iya tunawa a kwanan baya ne wasu Jihohi a yankin Arewa maso Yamma suka rika rubutawa ma’aikatar sadarwa ta kasa cewa suna neman bukatar a rufe layukan waya a wadansu kananan hukumomin da ake ganin akwai matsalar tsaro a yankin da nufin ba jami’an tsaro damar aiwatar da aiki bayan dakile matsalar masu bayar da bayanan ga yan Ta’adda.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.