Home / News / Kwamitin Sasanta Yayan APC Ya Isa Jihar Kano

Kwamitin Sasanta Yayan APC Ya Isa Jihar Kano

Mustapha Imrana Abdullahi

Kwamitin tabbatar da yin sasanci tsakanin yayan jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ya isa Jihar Kano inda har ya fara gudanar da zamansa a yau Asabar domin aiwatar da aikinsa na tsawon kwanaki uku.
Kwamitin karkashin jagorancin shugabansa Dokta Tony da kuma sakataren Kwamitin Dokta Aminu Waziri da suka yi jawabai da harshen Turanci da hausa, wato Dokta Tony ya gabatar da jawabin dalilin zuwansu Kano inda shi kuma Dokta Aminu Waziri ya yi jawabi kan abin da ya sa uwar jam’iyya ta aiko su Kano duk sun bayyana cewa sun zo ne domin yin aikin sasanci tsakanin yayan jam’iyyar APC kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadar, bayan sauraren korafin da ake da shi.
“Mun zo ne domin yin aikin sasanci bayan mun ji korafe korafe a tsakanin yayan jam’iyyar APC na Jihar Kano, kuma za mu yi aiki ne da abin da ke cikin kundin tsarin mulkin jam’iyya don haka duk abin da bashi a cikin kundin tsarin mulkin jam’iyya ba ruwan mu da shi”, inji Tony da Tambuwal
Dukkansu sun tabbatar da cewa bisa yadda aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC a dakin taro na Sani Abacha nan ne za su gudanar da aikin sauraren jin korafe korafen yayan APC, kuma bisa tanajin tsarin mulkin jam’iyya saboda haka duk abin da ya sabawa hakan ba ruwansu da shi.
Kamar yadda suka ce “ko a cikin gidan mutum ana iya samun sabani da Juna kuma haka lamarin yake a tsarin rayuwa, don haka za a iya sabawa kuma a zo a zauna a sasanta komai kamar yadda kowa ya Sani yayan APC duk uwa daya ne Uba daya”.
Kamar yadda shugaba da sakataren kwamitin suka bayyana cewa za su fara zama a yau Asabar har zuwa karfe hudu kuma gobe Lahadi kwamitin zai zauna sai ranar Litinin duk za su yi aiki kafin su rubuta rahotonsu.
Indai za a iya tunawa a satin da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC a matakin Jihohi wanda sakamakon hakan bangarori biyu duk suka gudanar da zabukansu kuma nan da nan aka rufa wurin uwar jam’iyya ta kasa da korafe – korafe, wanda sakamakon hakan ne aka nado kwamitin sauraren jin korafe korafe karkashin Dokta Tony domin ya saurari kowa a duk fadin Jihar Kano.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.