Home / Uncategorized / Muna Yin Kira Ayi Koyi Da Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal

Muna Yin Kira Ayi Koyi Da Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal

Ayi Koyi Da Gwamna Dauda Lawal Na Jihar Zamfara – Bashir Nafaru

Daga Imrana Abdullahi

An yi kira ga daukacin al’umma tare da shugabanninsu baki daya da su yi koyi da irin kokarin da Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ke yi domin samo hanyoyin warware dukkan matsalolin da ke addabar jama’a a koda yaushe.

Bashir Nafaru ne ya yi wannan kiran inda ya ce yin Zanga Zanga hakika ba shi ne mafita ba, don haka yin koyi da abin da Gwamnan Jihar Zamfara a karkashin Jam’iyyar PDP ya yi na tara malamai daga ko’ina cikin fadin Jihar ta yadda za a samu nasarar kawar da matsalolin da ke tattare da al’umma misali irin Barayin Daji,satar mama’s da dai sauransu.

Bashir ya ci gaba da kawo misali da cewa ” kamar irin yadda Sanata Abdul’Aziz Yari ma ya yi na tara al’umma na Jam’iyyarsa ya taimaka masu kuma ya shaida masu cewa bai amince ayi Zanga Zanga ba”.

Sai kuma bashir Nafaru ya yi kira ga ministan kasa a ma’aikatar tsaro Muhammadu Bello Matawalle da ya tuna da shi dan Maradun ne don haka ya dace lallai ya taimakawa jama’ar Jihar ta hanyar waiwayo wa tun daga garin Maradun zuwa sauran Jiha baki daya ya taimakawa mutane ya samar da ayyukan yi a dauki matasa, saboda a Jihar Zamfara hakika akwai karanci ayyukan yi, in ban da Allah ya kawo wannan bawan Allah Abdul’Aziz Yari ya lallashi jama’ar Jam’iyyarsa ya kuma ce za a yi abin da ya dace ayi lallai da Allah kadai ya san abin da zai faru na barnace barnace.

Don haka ne muke yin kira ga ministan Matawalle da ya yi amfani da damar da Allah ya bashi a dauki matasa aiki, a kuma taimakawa rayuwar al’umma ya zama an yi maganin cima zaune.

About andiya

Check Also

A Cikin Halin Bakin Ciki Da Kuncin Rayuwa A Najeriya

Wani mai gwagwarmayar kwato yancin al’ummar kasa da kuma fadakar wa Bashir Nafaru ya bayyana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.