Kamar yadda muke samun wadansu ingantattun rahotonnin daga jihar Borno, sun tabbatar da cewa mutane biyu sun gudu da ke jinya dauke da cutar Covid – 19 a jihar, kamar yadda kafar yada labarai ta TheCable ta ruwaito.
Mutum biyun sun gudu ne bayan gwajin da hukumar kula da Lafiya ta NCDC ta yi masu ya na tabbatar da suna kamu da cutar, inji Kwamishinan lafiya na jihar Salish kwayabura.
Kwamishinan yace ana zargin Abba Kaka Hassan mai shekaru 24, tare Hauwa Mohammed mai shekaru 42, da tserewa daga asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, bayan an tabbatar da suna dauke da cutar.