Home / KUNGIYOYI / Mutane Na Kara Nutsewa Cikin Wahala A Kaduna

Mutane Na Kara Nutsewa Cikin Wahala A Kaduna

Mutane Na Kara Nutsewa Cikin Wahala A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda wakilinmu ya zagaya cikin garin Kaduna, ya ganewa idanunsa tare da tambayar al’umma halin da suka shiga ciki sakamakon matsalar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da uwar kungiyar kwadago ta kasa ke gudanarwa a Jihar Kaduna baki daya.
Kamar yadda wakilinmu ya ganewa idanunsa a halin yanzu mutane na kara shiga cikin mawuyacin hali kasancewar tasirin da yajin aikin yan kungiyar kwadago ke aiwatarwa a Jihar.
Wadansu mutane a cikin unguwannin garin Kaduna sun shaidawa wakilinmu cewa su na cikin mawuyacin hali saboda ba wuta ba ruwan Famfo,asibiti,wutar lantarki duk babu duk gidajen mai sun rufe matsaloli na kara addabar jama’a, wanda sakamakon hakan ake sayar da ruwa jarka daya naira dari biyu kurar ruwan kuma guda daya naira dubu daya zuwa dubu da dari biyu da dari uku.
Kudin ababen hawa na haya mota Bus daga kasuwa zuwa Kawo naira dari da Hamsin zuwa dari 200, kudin Keke Nafef daga dari da Hamsin zuwa dari biyu.
Sai kuma kudin fetur inda ake sayar da Galan guda har naira dubu da dari biyu ko saye ko saye ga kuma yawan hau hawar farashin kayan masarufi da komai a yanzu farashinsa yake kara kudi sakamakon tsananin da komai ya yi saboda yajin aikin da yan kwadago ke aiwatarwa a halin yanzu.
A yau rana ta biyu da yan kungiyar kwadago ke Zanga zangar yajin aiki inda suka tashi daga ofishin kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna zuwa shatalai talan da ke kusa da babban ofishin kula da al’amuran wutar lantarki na shiyya da ke kan titin Ahmadu Bello a Kaduna.
A lokacin da yan kungiyar kwadagon suka yi sansani a shatalai talan Ahmadu Bello cikin garin Kaduna ne aka samu wadansu matasa zauna gari banza suka zo a wasu motoci wasunsu dauke da Gorori da wukake su na kokarin farwa mahalarta taron kungiyar kwadagon da suke yin jerin Gwanonsu cikin lumana.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.