Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Al’ummar da ke zaune a karamar hukumar Funtuwa cikin Jihar Katsina sun bayyana cikakkiyar gamsuwarsu da irin yadda Gwamnatin tarayya karkashin Muhammadu Buhari ke kokarin kawar da yan ta’addan da ke addabar jama’a.
A wani binciken jin ra’ayin jama’a da wakilin mu ya gudanar a garin na Funtuwa game da daukewar layin wayar sadarwa na MTN, jama’ar sun bayyana cewa koda an yi hakan ne domin kokarin da ake yi wajen kawar da yan Ta’adda hakika su na goyon baya da nuna cikakken hadin ga dukkan matakan Gwamnati uku.
Jama’ar dai sun bayyana cewa ai daman Gwamnati tuni ya dace ta dauki wannan mataki a kan yan ta’addan da ke kokarin hana Noma,karya tattalin arzikin kasa ta hanyar satar mutane su na karbar kudin fansa domin son zuciyarsu kawai.
“Muna yi wa Gwamnatin Najeriya fatan samun nasara mai dorewa a kan wadannan yan Ta’adda marasa kishin kasa”, inji jama’a.