Home / News / Na Fito Talara Ne Domin Yi Wa Jama’a Aiki- Isa Kwankwasiyya

Na Fito Talara Ne Domin Yi Wa Jama’a Aiki- Isa Kwankwasiyya

Na Fito Talara Ne Domin Yi Wa Jama’a Aiki- Isa Kwankwasiyya
Mustapha Imrana Abdullahi
Mai Neman Jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar kujerar shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa a cikin Jihar Kaduna jigo a darikar Kwankwasiyya Alhaji Isa Abdullahi ( Balarabe), ya bayyana batun takararsa a matsayin hidima ga jama’a.
Alhaji Isa Abdullahi, ya bayyana wa taron mutanen da suka tilasta masa tsayawa takarar cewa ya fito neman wannan takara ne da amincewar jama’ar mazabarsa da suka ga dacewarsa ya tsaya takarar.
“Bisa wannan dalili ne da jama’a suka ga dacewar ayi wannan takara yasa na amsa kira, saboda haka nake gayawa jama’a cewa lamarin wannan takarar ba abin a mutu ko ayi rai ba ne”.
Saboda haka nake yin kira ga daukacin yayan jam’iyyar PDP a duk inda suke cewa su hada kansu su tabbatar da Kaunar Juna domin ayi tafiya tare.
” Duk wanda ya san akwai wani dan kaikayi a tsakaninsa da wani ya dace a samar da maslaha domin babu hamayya tsakanin yayan PDP a kowane irin mataki, kowa ya dace ya Sani abokan hamayyar neman nasara su ne wadanda suke a wata jam’iyya amma ba yayan PDP ba”.
Isa Kwankwasiyyar ya kuma tabbatarwa al’umma mazabar Kaduna ta Arewa, Jihar Kaduna da kasa baki daya cewa takararsa aiki ne na yi wa jama’a hidima ta yadda za a samu ci gaban kasa baki daya.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.