Home / Kasuwanci / Na Karu Kwarai Da Abin Da Bankin Nexim Ke Yi – Mustapha Habib

Na Karu Kwarai Da Abin Da Bankin Nexim Ke Yi – Mustapha Habib

 Imrana Abdullahi
Alhaji Mustapha Habib dan kasuwa ne da ke shugabancin kamfanin Dutse Granite,ya bayyana irin yadda Bankin Nexim ke yi na fadakarwa domin masu shigowa da fitar da kaya kasashen waje abin a ya ba ne kasancewa hanyar karuwa ce kamar yadda shi da kansa ya karu da taron bitar.
Mustapha Habib ya ci gaba da cewa “Hakika ya Gamsu da irin abin da Bankin Nexim ke yi domin fadakar da jama’a yadda za su amfana ta fuskar shigowa da fitar da kayayyakin da ba Man fetur ba kasashen waje, saboda haka ne ya sa na halarci wannan taron na su don ni ina da masaniyar dabarun  me zan yi na dabarun abin da nake yi, to, domin Bankin Nexim ba da sai dai in mutu da dabaru na kawai “
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron bitar da Bankin Nexim ya shirya wa masu kamfanoni da kokarin shigowa da kaya da kuma fita da kayan da ba man fetur ba kasashen waje, inda ya ce ya Gamsu da cewa babu abin da kasar Nijeriya ba za ta iya yi ba, don na san Allah ya albarkace mu da wadansu abubuwa kwarai na ci gaba ta fuskar tattalin arziki sai dai sakaci kawai irin na mu a kasa mayar da hankali ayi amfani da albarkar da Allah ya yi mana, saboda haka ina da yaya injiniyoyi hudu ne a gidana, ina da masu ilimin zayyanar gine gine guda biyu ina kuma da akanta duk a gidana to, ana samun masu kammala makaranta a kullum ta yaya Gwannati za ta iya daukar nauyin jama’a har ta ba su aikin yi, don haka dole ka yi abin da zaka bar wa bayan ka bisa wannan dalilin ne ya sa nake yin abin da nake yi a yanzu.
Mustapha Habib ya kuma bayyana irin gamsuwar da yake da ita ta fuskar samun kasuwa, domin ya ce sana’ar da yake yi kafin ma ya kammala har ya sayar da kayansa kuma a nan cikin gida yake samun kasuwarsa.
Don haka ne ya ce a yanzu haka akwai wanda yake bukatar zai sa yi kayansa a kasar Ghana amma da can bai san yadda zai yi ba, amma a yanzu da ya halarci taron bitar Bankin Nexim komai ya warware a wurinsa ya samu masaniyar yadda zai yi wajen fitar da kayansa kasashen waje.
“Saboda haka abu ne mai kyau mu yarda da kanmu, kuma mu amince da kasar mu, my san cewa babu wanda zai gyara mana sai mu da kan mu, don haka duk wani da zai zo ya na yi maka turancin kasashen waje duk ba gaskiya ba ne, mu kadai ne za mu iya gyara kan mu da kan mu kawai in mutum na zancen waje mutum na yaudarar kansa ne kurum wannan Bankin na Nexim a yanzu ya na taimaka mana saboda a can baya mutane ne daga kasashen waje ke zuwa daga su sai Jaka amma sai ya zo ya mallaki mutane ya rika juya mutanen mu “ni daga Kano nake akwai wasu mutane da suke a Kano ba su san komai ba amma sai su mayar da jama’a Leburori, to yanzu Allah ya ba mu ilimi da basira ba abin da ba za mu iya yi ba a kasar mu sai dai idan mun sa lalaci da karayar zuciya kawai.
Mustapha Habib ya ce sana’ar da yake yi a yanzu da bai ko cika shekara daya da farawa ba amma ana ta Gogawa da shi domin Dutse ne zai yanka ya goge shi ya wanke ya yi masa irin zanen da yake bukata kuma ana samun ci gaba kwarai har ma ya na gogawa da wadanda suka dade su na yi shi ko a kasa da shekara gida kawai ana ta fafatawa da shi.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.