Home / Kasuwanci / Mune Kan Gaba Wajen Daukar Ma’aikata – Dangote

Mune Kan Gaba Wajen Daukar Ma’aikata – Dangote

Mustapha Imrana Abdullahi
….Bayan Gwamnati Sai Kamfanin Dangote
Rukunin kamfanonin Dangote ya bayar da gagarumar gudunmawarsa wajen ci gaban tarayyar Nijeriya sakamakon bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma samar da aikin yi ga dimbin jama’a.
Alhaji Ahmed Hashim ne ya bayyana hakan lokacin da ya wakilci babban Daraktan kamfanonin rukunin Dangote a lokacin baje kolin kasuwar duniyar kasa da kasa karo na 42 a Kaduna.
Alhaji Ahmed Hashim ya ci gaba da cewa kamfanin na kokarin bunkasa Noman Alkama a Najeriya.
“Mu ne wadanda muka fi kowa daukar mutane aiki bayan gwamnati. Don haka muna kokarin bunkasa Noman Alkama da kuma sarrafa ta duk a kokarin mu na ganin mun bayar da aikin yi ga mutane a kalla 107,000 a kamfanonin mu na rake da kuma kamfanin Shinkafa”, inji shi.
Ya ci gaba da cewa ” dukkan manyan motocin kamfanin Dangote da kuke gani suna kan tituna a cikin kasar nan, ana harhada su ne a Najeriya tare da hadin Gwiwa da Najeriya da kamfanin Sino tricks”.
Alhaji Hashim ya ci gaba da cewa kamfanin Dangote da hadin Gwiwar Gwamnatin Jihar Kaduna tuni su na nan su na gina wa da kuma Farfado da kamfanin motocin Fijo (Peugeot automobile limited) a Jihar kaduna.
Tun farko a jawabinsa, Janar Manajan Shiyya mai kula da harkokin Sayarwa da kuma tallatawa a yankin Kaduna, na takin kamfanin Dangote, Mista Agbana Isaac Oladele cewa ya yi kamfanin ya kirkiri wani bangare da aka Dorawa alhakin duba yanayin kasa a kuma aunata a dakin Gwaje Gwaje domin tabbatar da yadda take a samar da Takin da ya dace da ita.
Ya ce wani bangare na abin da kamfanin Takin ke bukata shi ne ya taimaka wajen samar da ingantaccen Takin zamani ga kasa domin a samu wanda ya dace da kowace, kuma yin haka zai bayar da damar a kaucewa irin yadda lamarin yake a can baya da ake samar da taki kala guda ga dukkan kasa wanda ba lalle ba ne ta na bukatarsa ba.
Ya kara da cewa “bangaren bunkasa harkokin kasuwanci ma wani bangare ne daban da ke kunshe da dimbin masana harkokin Noma da za su rika horar wa da ilmantar da manoma ta hanyar yin tarurruka da manoma”.
Da yake jawabi, Manajan shiyya, na yankin Arewa ta tsakiya, mai kula da sayar da Gishiri da kayan dandanon abinci, mists Solomon Adeoye, cewa ya yi rukunin kamfanonin Dangote ya samu nasarar sayen hannun jarin kamfanin NASCON Allied Industry Plc na kashi 70 kuma sun dade su na samar da Gishori da kayan dandanon abinci tun da suka sayi kamfanin na NASCON.
Ya ci gaba da bayanin cewa Gishirin da kamfanin ke samarwa dauke yake da dukkan sinadarin bitamin da ke taimakawa wajen yara su girma ba tare da samun wata matsalar lafiyar hankali ba.
Ya ce sinadaran dandanon Girki da kamfanin ke samarwa guda biyu su ne ‘Dangote Quality Seasoning da Dangote Classic Seasoning’.
Ya kara da cewa ban da samar da Gishiri domin amfani a gidaje da kuma amfani da shi a kamfanoni, sai ya kara da cewa an kuma bude wani sabon kamfani a Jihar  Legas wanda zai taimaka wajen samawa jama’a irin Gishirin da ake bukata na amfanin jama’a da yawa.
A nasa bangaren, Manajan Sayarwa da ke kula da Arewa ta tsakiya, da ke Kaduna mai kula da sayar da Siminti,Alhaji Mustapha Yelwa cewa ya yi ” muna da fiye da masu sayen simitin sama da dari uku (300) da suke saye su kuma rabar da shi a cikin kasa baki daya”.
Ya kara da bayanin cewa a matsugunnan kamfanonin Dangote guda hudu su na samar da tan miliyan Talatin da uku na siminti ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a kan irin yadda karfin kamfanonin yake na abin da suke samarwa.
Ya ce kamfanin Obajana na Jihar Kogi da ke samar da Siminti na samar da tan miliyan sha biyar (15), kuma kamfanin Siminti na Ibeshe na samar da Siminti tan miliyan sha biyu (12) kamfanin da ke Gboko a Jihar Banuwai na samar da tan miliyan hudu (4) shi kuwa kamfanin da ke OK Pella a Jihar Edo na samar da tan miliyan sha biyu (12).
A kasuwar baje kolin kasa da kasa ta Kaduna karo na 42 rukinin kamfanin Dangote sun baje kolin dukkan wadannan kayan da muka lissafa da kamfanoninsu ke samarwa.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.