Related Articles
Daga Sani Gazas Chinade, Azare
Shugaban riko na karamar hukumar Katagum a Jihar Bauchi, Alhaji Musa Ahmad Azare, ya bayyana kyakkyawan kudirinsa na gudanar da aiki tukuru ga al’ummarsa da dan abin da ake ba shi na kason wata-wata duk da irin girman da karamar hukumar ke da shi a matsayin ta karamar hukuma ta biyu a girma a jihar Bauchi.
Alhaji Musa Azare ya bayyana haka ne ga wakilinmu a garin Azare jim kadan da dawowar sa daga duba aikin gina hanyar da ta hada kasuwar Azare da babban titin Kano zuwa Maiduguri wadda ambaliyar ruwa da ake shekawa a wannan damina ya yi aure ya tare a wajen na tsawon watanni da ya zama alakakai ga ‘yan kasuwar da ke kawo kayayyakin su daga kowane sashi na yankin da ma jihohin makwabta.
Shugaban rikon karamar hukumar ya cigaba da cewar, ita wannan hanya tsawon ta ya kai kimanin kilomita 1.5 wadda ya bada aikin ta don zuba mata jar tsakuwa matsayin daukin gaggawa wadda hakan ne dai-dai da aljihun karamar hukumar daga bisani kuma ina da yakinin In Allah ya so gwamnatin Jihar Bauchi karkashin mai girma gwamna Bala Abdulkadir Kauran Bauchi za ta zuba kwalta akai.
Da Wakilinmu ke tambayar sa akan ko me ya jawo hankalin sa don gyara wannan hanya a matsayinsa wadda duka-duka bai wuce ‘yan kwanaki ba akan mulki? “Anan sai ya amsa da cewar, Ai a lokacin da aka kawo ni don jagorantar wannan karamar hukumar ta mu mai albarka sai na kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Katagum Dr Umar Faruq Kabir Umar a faduwar sa, to anan ne mai martaba da kan sa ya nemi da na kokarta don gyara wannan hanya da ta shiga sabuwar kasuwsar ta Azare lura da cewar ruwa ya mamaye ta babu ta yadda za ka iya shiga da dadin rai, to shine na kudurta hakan da dan abin da nake samu, Allah kuma ya sa na kai ga nasarar yin hakan.”
Daga nan sai shugaban ya tabbatarwa al’ummar karamar hukumar da cewar, ya shirya tsaf don ganin ya gudanar da ayyukan da al’ummar ke da bukatar su da dan abin da ya ke samu ba tare da yin kasa a gwiwa ba duk da yawan al’ummar da karamar hukumar ke da shi.
Ya kuma nemi al’ummar karamar hukumar da su ba shi goyon baya don ganin ya samu damar musu hidima a matsayin sa na shugaba kuma dan su wadda matukar ya samu hakan da yardar Allah za su ga ‘yan canje-canje fiye da kima.
Shugaban ya kuma tabbatarwa da al’ummar cewar lalle shi mamba ne a jam’iyyar PDP da ke mulkin Jihar to amma su Sani cewar shi a yanzu shugaba ne na kowa .
Don haka a shirye ya ke da ya rungumi kowa ba tare bambanci ba, domin karamar hukumar Katagum tamu ce duka.
Daga nan ya ja hankalin Matasan nan da ke da halayyar tada hankalin jama’a da su yi watsi da irin wannan mummunar akida domin kuwa babu alkhairi cikinta illa nadama, su dawo su zama mutane nagari a matsayin su na manyan gobe wadda a shirye gwamnati ta ke don ganin ta dafa musu don kama sana’o’in dogaro da kai.
Shugaban ya kuma jajantawa magidantan da a kwanakin baya ‘ya’yan su biyu suka rasu a garin Azare a sakamakon cin wata doyar Rogo da ke dauke da wani sinadari mai illa, ya yi fatan Allah jikan su da rahama su kuma mutanen da suka jikkata a wancan lokacin sakamakon cin wannan rogo Allah ya kara musu lafiya ya kuma kiyaye faruwan irin ya hakan nan gaba.