Home / News / Nazo In Dawo Da PDP Kan Karagar Mulki Ne Ba Wawurar Kudi Ba – Ayu

Nazo In Dawo Da PDP Kan Karagar Mulki Ne Ba Wawurar Kudi Ba – Ayu

…Jam’iyya Za Ta Wallafa duk kudin da ta samu da yawan abin da aka kashe a watan Disamba
Biyo bayan irin yadda ake ta kace- nace a tsakar gidan jam’iyyar PDP musamman ma a matakin jam’iyyar na kasa ya sa shugaban PDP na kasa Dokta Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa an zabe shi ne domin yin aikin samar da nasarar jam’iyyar zuwa madafun iko a tarayyar Najeriya, ba wai kwashe dukiya ko yin watandar  kudin jam’iyyar ba.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun Simon Imobo-Tswam, mai bayar da shawara na musamman ga shugaban PDP na kasa a kan harkokin kafafen yada labarai da sadarwa.
Ya kuma bayyana cewa tuni ya bayar da umarni ga bangaren kudi na ofishin jam’iyyar da a koda yaushe su rika tabbatar da ainihin kididdigar kudin da suka shiga asusun jam’iyyar da kuma abin da aka kashe a kuma bayar da cikakken rahoto ga babban kwamitin shugabannin jam’iyyar na kasa a lokacin bikin shekara daya a karagar mulkin babban kwamitin na kasa da za a yi a watan Disamba.
Takardar da ce wannan kalamai ne suka kasance maganar shugaban PDP na farko a bisa zargin da aka yi masa a kafafen yada labarai a kan batun cin hanci da rashawa da bayar da kudi ta hanyar da bata dace ba ga yayan jam’iyyar musamman ma yan kwamitin Zartaswa na jam’iyyar.
Ayu ya ci gaba da cewa zai iya samun kurakurai a matsayinsa na dan Adam, amma dai satar kayan wani ko wasu ba shi daga cikin kuskuren da zai yi,saboda haka babban kwamitin Zartaswa na jam’iyyar da ke aiki a halin yanzu suna yin aiki ne bisa doka da ka’ida.
Ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake maraba da zababbun masu jagorancin jam’iyyar suka kawo masa ziyarar ana tare a hedikwatar jam’iyyar ta kasa.
Kamar yadda kalamansa suke: “Jam’iyyar PDP ba wai an samar da ita ba ne domin ta zama jam’iyyar adawa. Mun samar da ita ne domin ta samu mulki a ciyar da kasa gaba. Don haka ina son in kasance cikin tarihi ya zamo cewa na mayar da jam’iyyar a kan karagar mulki. Ba wai zan zamo shugaban PDP na har abada da. Saboda haka abin da na Sanya a gaba shi ne in dawo da PDP a kan karagar mulki. Ba nazo domin in yi satar kudi ba ne. Ina da kyakkyawan tarihin aikin Gwamnati da na yi kuma ya na nan.
“Na taba zama shugaban masu rinjaye a majalisar kasa. Na kuma zama minista a lokuta da dama. A matsayina  na mutum, ina da kura kurai, amma dai batun yin sata bashi daga ciki. Ina da yakinin hakan a duk inda na yi aiki domin ina da tarihi, don haka shugabancin jam’iyyar da nake yi a halin yanzu ya san abin da ya dace ayi ta fuskar kiyaye doka da ka’ida musamman a kan al’amuran da suka shafi kudi da shugabanci.
“Zaku iya karanta abubuwa da yawa da ake tsammanin ji daga baki na. Idan ba ma yin magana a koda yaushe, hakan na faruwa ne domin muna son a koda yaushe a ci gaba da samun kyakkyawar dangantaka a tsakanin yayan jam’iyya.Ba wai a kida yaushe a rika jin cece- kuce a tsakanin yayan jam’iyyar PDP ba. Domin muna son samun nasara ne a lokacin babban zaben shekarar 2023 mai zuwa”.
“Saboda haka ba mu son kaucewa daga wannan tsarin. Don haka ya dace mu yi duba sosai da idanun basira. Domin duk wani abu sai zo a kashi na biyu ne. Mun shigo wannan ofishi ne saboda akwai matsalar rigima a cikin jam’iyya.
Kuma ba mu son mu ci gaba da tafiya cikin matsalar rikici. Domin hakan ba zai yi wa jam’iyya dadi ba.Ba za mu zauna a cikin rikici da Juna ba,musamman a inda ya kasance cewa rikicin kirkirarsa aka yi.
Ya kara da cewa: “Babban kwamitin Zartaswa na kasa ya zauna tare da tattauna batutuwan da suka shafi bayar da kudin alawus alawus na gida. Kuma duk gida ya amince a wajen taron cewa ba wani batun cin hanci ko wani lamarin rashin gaskiya da ya faru.Kuma tuni aka fitar da takardar bayanin komai dalla- dalla ga manema labarai.Kuma an kammala maganar tuni”.
Tun da farko shugaban tawagar, Honarabul Yunana Iliya, cewa ya yi sun zo hedikwatar ne domin bayyana cikakken hadin kansu da goyon baya ga shugaban PDP na kasa, da kuma yi masa alkawarin ci gaba da yi wa Ayu da ke jagorantar shugabancin masu zartaswa biyayya.
“Saboda haka muna tabbatar maka da cewa mun kada maka kuri’ar goyon baya da kuma ana tare, domin haka muna yin kira ga daukacin yayan jam’iyya da su ci gaba da mika wuya don a ta fi tare wajen yi wa jam’iyya aiki a samu nasara”, ya kara da bayanin hakan.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.