Shaikh Sani Yahya Jingir, sanannen Malamin addinin Musulunci ne kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar Izala reshen Jos assasawar marigayi Malam Sama’ila Idris ya bayyana cewa shi Honarabul Isa Ashiru Kudan ne zabinsa kuma shi zai zaba domin ya zama Gwamnan Jihar Kaduna.
Shaikh Sani Yahya Jingir ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon murya da hadimin Isa Ashiru Kudan suka aikewa wakilinmu.
Shaikh Sani Yahya jingir ya ce hakika babu wata tantama Isa Ashiru ne zai zaba domin ya zama Gwamnan Jihar Kaduna a zaben shekarar 2023 da za a yi ranar 11 ga watan Maris.