Home / News / Olawepo-Hashim Ya Gargadi Masu Rura Wutar Kabilanci, Ya Bayar Da Mafita A Kan Zaman Lafiya

Olawepo-Hashim Ya Gargadi Masu Rura Wutar Kabilanci, Ya Bayar Da Mafita A Kan Zaman Lafiya

Olawepo-Hashim Ya Gargadi Masu Rura Wutar Kabilanci, Ya Bayar Da Mafita A Kan Zaman Lafiya
 Mustapha Imrana Abdullahi
Domin a samu ingantacciyar rayuwa ga kowa, ya zama wajibi yan Nijeriya su hanzarta yin watsi da batun bambance bambance a tsakaninsu musamman ta hanyar yin amfani da kalaman da ba su dace ba.
Dan kasuwa wanda ya yi takarar shugaban kasa a shekarar 2019 Mista Gbenga Olawepo- Hashim ya bayar da shawarar.
Da yake magana a game da irin yadda ake samu batutuwan Rabe raben kawunan jama’a a kan kabilanci a Nijeriya, Hashim ya bayyana cewa yin maganganu a kan wata kabila ana Dora Mata laifi a kan wata domin kawai a Sanya wasu su rika yin ramuwar gayya ba zai haifarwa kasar da mai ido ba don za a iya samun lalacewar al’amura.
A cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai a Abuja, Mista Olawepo- Hashim, wanda ya nuna damuwa kwarai a kan al’amarin, ya ce lamarin da ke tsakanin manoma da makiyaya wanda ya dade shi ya haifar da matsalar tsaron da ake ciki a halin yanzu, saboda haka bai dace wasu mutane su rika kokarin nuna kamar yanzu ne matsalar ta faru ba, domin hakan zai iya hassala wadansu har su fusata lamarin ya zama tamkar bambancin irin na kabila.
“Duk mai son Nijeriya lallai zai damu kwarai. Ni na damu.Dukkanmu muna da abin da zamu iya yi, shugabannin al’umma da kungiyoyi masu zaman kansu ya dace su yi dukkan mai yuwuwa a samu mafita”, inji shi.
“Yanzu lokaci ya yi da za a kara karfafawa hukumomin tsaro domin su aiwatar da aikinsu kamar yadda ya dace.Kuma yanzu lokaci ne da shugabannin Gwamnati za su yi aikin da zai nuna cewa lallai su shugabanni ne.Dole my hada kai domin mu kubutar da kasa”, Olawepo – Hashim ya ce haka.
Kamar yadda shahararren dan kasuwar ya bayyana,”shugabanni a kowane irin mataki dole su kaucewa yin kalamai da aiki a aikace da zai nuna goyon baya ga duk wani bangare game da tashin tashina, domin zai iya haifar da matsala a batun zama kasa daya al’umma daya da kuma harkar tsaro.
“A kan matsalar fadace fadace a tsakanin Makiyaya da Manoma a ko’ina a fadin Nijeriya kuwa, dukkan yan kasa nagari da suka hada har da shugabanni  sun amince duk wani lamari na kiwo da zai iya haifarwa wani matsala a kan kasuwancinsa ko harkarsa, to a bar shi domin ayi amfani da hanyoyin zamani a samu ci gaban da kowa ke bukata”.
“Muna son samun tsarin Gwamnati Gwamnati wata zuwa wata da zai hada tare da biyan bukatar talakawan manoma da makiyaya da Gwamnatoci da dama da suka gabata suka yi. Wannan lamari ne da ake matukar bukata a gaggauce domin samun tsari tun daga Gwamnatin tarayya zuwa matakin Jiha.Mai yuwuwa wannan lokaci ne zamu sake jaddada kiraye kirayen da muka yi na a samawa Jihohi wani iko a bangaren kula da tsaro da kuma wadansu abubuwa masu sarkakiya, domin a samawa Gwamnatin tarayya sauki wajen gudanar da aikin Yan Sanda”, ya ce.
Ya kara jaddada cewa tsarin aikin tsaron na Yan Sanda a jihohi da kananan hukumomi zai taimaka wajen rage matsalar kamar dai yadda ake bukata a koda yaushe a samu dauki na gaggawa kafin lamarin ya zama wata matsala da za ta shafi kasa baki daya, domin a samu wadansu jami’ai masu karfi su shiga lamarin zundum.
In zaku iya tunawa Olawepo- Hashim ya bayyana a cikin wata tattaunawar da ta gabata cewa yana da kyau yan Nijeriya su amince da abubuwan da za a iya amincewa da su sannan kuma a ci gaba da tattaunawa a kan wadansu abubuwan da ba su zama an amince da su ba amma za su iya zama an amince da su a nan gaba sakamakon tattaunawar.
Nijeriya, ya ce, dole su zauna cikin zaman lafiya da taimakon Juna.
Kuma ya bayyana cewa samun ingantacciyar kasa ba abu ne da za a iya samu a kwana daya ba, dan kasuwar ya kara fayyacewa jama’a cewa akwai ci gaban rayuwa bayan shekarar 2023 kuma Nijeriya za ta ci gaba da zama kasa daya al’umma daya.
Kuma za a iya duba wadansu abubuwa bayan zaben shekarar 2023 da ikon Allah, ya ce.
Dan kasuwar da ya zama dan siyasa ya bayyana cewa daga cikin irin mahawarar da ake ta yi zai zama dole sai an cimma wata matsaya a kan wasu batutuwa Lamar samar da yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro,raba madafun iko zuwa ga Jihohi domin su rika sarrafa ma’adinai da suke a yankunansu sai su rika biyan haraji ga Gwamnatin tsakiya.
Ya bayyana wadansu wurare da akwai ainihin batu a bayyane na dai- daitawa a tsakanin Juna na kirkiro da yan sandan Jihohi da kananan hukumomi da suke tafiya kafada da kafada da Yan sandan Gwamnatin tarayya  da nufin kara karfafa harkar aikin dan Sanda ta inganta kuma a samu karin ingantawar harkokin tsaro da dai sauransu.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.