Related Articles
Rundunar Yan Sandan Katsina Sun Kama Kasurgumin Dan Ta’adda
Imrana Abdullahi
Rundunar yan sanda ta kasa reshen Jihar Jihar Katsina sun yi nasarar kama wani kasurgumin dan Ta’adda mai satar mutane da ke Dajin Rugu a karamar hukumar Safana ta Jihar Katsina.
Kamar yadda mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isa ya bayyana a cikin wata takarda mai dauke da sa hannunsa cewa wanda ya shiga hannun rundunar mai suna Abubakar Ibrahim dan shekara 19 Alhaki ne ya kama shi na irin abin da yake aikatawa inda da kansa ya yi batan kai sai gashi a wurin jami’an yan sanda masu yaki da yan fashi wato SARS.
Kamar yadda takardar Gambo Isa ta bayyana cewa wanda ya shiga hannun na cikin gungun masu satar jama’a domin neman kudin fansa da suka addabi kananan hukumomin Safana, Batsari, Dan Musa da Kurfi duk a Jihar Katsina.
Wanda aka kaman ya jagoranci wadansu masu satar jama’a yan uwansa a kan Babura dukkansu dauke da bindigar AK 47 sun kai hari kauyen Dagarawa da Kudewa duk a cikin karamaar hukumar Safana sun kuma sace wani mai suna Ashoru Ibrahim mai shekaru 32 a kauyen Dagarawa cikin karamar hukumar Safana da Kurdi sai wacce aka sace ta biyu mai suna Duduwa Audu Audu shekaru 50 da kuma ta uku Asiya Sale mai shekaru 45 duk a kauyen Kudewa a karamar hukumar Kurfi cikin Jihar Katsina an dauke su zuwa cikin Dajin Rugu.
Amma cikin ikon Allahbsai Alhaki ya kama wanda ya shiga hannun jami’an yan sandan yaki da yan fashi na SARS bayan ya karbi kudi naira dubu 241,000,000
a matsayin fansa daga hannunnyan uwan wadanda suka sace.
A lokacin da jami’an tsaron ke gudanar da bincike wanda aka kaman ya tabbatar da aikata wannan aikin shi tare da wadansu mutane da suka tsare a halin yanzu amma ana cikin nemansu duk baki daya.
Kuma an samu kudi a wurin wanda aka kama da suka kai naira dubu dari 241,200:00 a wurinsa.
A yau ranar 10 ga watan 9, 2020 rundunar ta samu nasarar kubutar da wadanda aka sace da muka aka ambaci sunayensu a baya an kuma hada su da yan Uwansu bayan an duba lafiyarsu a babban asibitin Kurfi na Gwamnatin Jihar Katsina, kuma ana ci gaba da bincike.