Home / News / Sakacin Buhari Ne Kasa Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya – Iyorchia Ayu

Sakacin Buhari Ne Kasa Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya – Iyorchia Ayu

Sakacin Shugaban Kasa Buhari Dangane Da Magance Matsalar Tsaro A Najeriya, Ishara Ce Dake Da Darasi A kan Bai Iya Samarwa Yan Najeriya Makoma Mai Kyau”

Inji Sanata Iyorchia Ayu
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa

 

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya baiyana rashin gamsuwa tare da damuwa a kan yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake watsi da muhimman shawarwari na samarwa Nijeriya mafita da rashin daukar mataki na ceto rayuka da dukiyoyin al’umma da ke salwanta Dare da rana a cikin kasa.

 

Bayanin hakan ya fito ne daga Ofishin Kwamitin Watsa Labarai na Sanata Iyorchia Ayu Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, da aka rabawa manema labarai.

 

Sanata Iyorchia Ayu ya fadi haka ne  a garin Makurdi ta jihar Binuwai a lokacin gudanar da taron murna wanda gwamnati da al’ummar jihar Binuwai karkashin jagoranci Gwamnan jihar Mista Samuel Ortom suka shirya masa.

 

 

Sanata Iyorchia Ayu yace, hakika ko shakka babu, sakacin Shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da dacewa ya dauki matakai masu tsauri don kawo karshen matsalar tsaro da sauran kalubale na daga cikin dalilan da zai sanya yan Nijeriya su amince da Shugaban Kasa bai da dubara ko karfin halin gyaran Matsalar kasarnan.

 

 

Kisan gilla na ganganci da cin amana irin wanda aka yiwa wasu mutane a Sokoto da na Kaduna da kisan Kwamishina a mahaifar shugaban kasa dake Katsina da wasu sauran hare-hare na fitar hankali da akeyi ana satar jama’a ko yi ma mata fyade da sauran irinsu duk na tabbatar da rashin adalci, da iya jagoranci na Shugaban Kasa Buhari da wadanda ya baiwa amanar kiyaye rayukan al’umma.

 

 

“Dole ne mu gaya ma Shugaban Kasa cewar, ya tashi tsaye ya rufe ido, ba sani ba sabo, yayi gyara akan matsalar da kasa take ciki; domin kuwa ana daukar rayuka al’umma ana kisan gilla tamkar kiyashi, abin da ya sanya tsoro da fargaba da rashin tabbas a zukatan al’umma, mussaman talakawa wadanda basu ci basu sha ba” Inji Sanata Iyorchia Ayu.

 

 

Haka ma ya roki yan Nijeriya da kada su karaya ko cire zullumi akan sake gina kasa mai albarka da Nagarta da zaman lafiya, muddin aka samu kyakyawan shugabanci nagari mai gaskiya da adalci ga al’umma.

 

Yace, kuskure ne ayi zancen wargajewa Nijeriya saboda wadanan kalubalen, don kuwa jam’iyyar PDP tana iya kokarin da take yi na sake ceto da gina kasa don amfani al’umma a gobe da zasu cimma burinsu na tabbatar zaman lafiya da rayuwa mai albarka da adalci.

 

 

Ya roki al’umma da su ci gaba da yi wa Nijeriya fatan alheri da neman hadin kai da uzuri ga lamuran da za su kara karfafa gaskiya, zaman lafiya da fahimtar juna a tsakani.

 

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.