Related Articles
MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Sanata Attai Idoko Ali da ya jagoranci zaben mataimakin shugaban jam’iyyar PDP shiyyar Arewa maso Yamma ya bayyana Sanata Bello Hayatu Gwarzo a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 426.
Yayin da wanda yazo na biyu Ibrahim Jamo ya samu kuri’u dari uku da sha uku 313
Sanata Attai Idoko Ali, ya yi godiya ga daukacin yayan jam’iyyar da duk wanda ya bayar da gudinmawa aka samu nasarar kammala zaben cikin kwanciyar hankali da lumana da suka hada da jami’an tsaro da yan jarida.