Home / Kasuwanci / Sanata Wamakko Ya Bukaci Jama’a Su Bunkasa Noma Da Samar Da Masana’antu

Sanata Wamakko Ya Bukaci Jama’a Su Bunkasa Noma Da Samar Da Masana’antu

Daga Imrana Abdullahi
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga daukacin yan Najeriya da su mayar da hankali a kan batun bunkasa Noma da samar da masana’antu da nufin bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasa.
Dan majalisar Dattawa Wamakko ya yi wannan kiran ne a Sakkwato a lokacin da ya kai ziyara ta kashin kansa a wani kamfanin sarrafa Shinkafa mai suna K,K Technology, wanda wani dan asalin Jihar Sakkwato, Alhaji Kabiru Mu’azu Jodi ya kafa
Wamakko Wanda ke wakiltar mazabar dan majalisar wakilai ta Sakkwato ta Arewa ya tabbatarwa da jama’a cewa mayar da hankali a kan bunkasa Noma da kakkafa masana’antu zai taimakawa bunkasar tattalin arziki a kasa kuma hakan zai taimaka wajen bunkasa kasar baki daya.
Wamakko ya bayyana cewa akwai bukatar samun muhimman kayayyakin bunkasa harkokin Noma da kuma aiwatar da Noman ta yadda za a samu wadataccen abinci a kasa baki daya.
“Muna da yawan jama’a, kasar Noma da kuma kwarin Gwiwar samun ingantaccen tattalin arzikin kasa, wanda hakan yasa ya jinjinawa kokarin da Alhaji Jodi, ya yi na samar da wannan kamfanin da ya bunkasa harkar Noma da samar da ayyukan yi ga jama’a ta hanyar masana’antar”.
Sai Wamakko ya shawarci jama’a kan bukatar da ake da ita na samun wadansu kamfanonin da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa da harkar Noma.
” Zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma samar da ayyukan yi a kuma samu magance matsalar rashin tsaro da kuma rage matsalar talauci a kuma samar da abin dogaro da kai a matsayin kasa mai kokarin samun ci gaba,
 Wamakko ya kuma bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Jiha za ta taimakawa wajen sayen kayan kamfanin a matsayin kara masa kwarin Gwiwa Wanda hakan zai Sanya wadansu ma su kafa kamfanoni a Jihar.
Tun da farko, Alhaji Jodi, ya shaidawa Sanata Wamakko cewa kamfanin ya fara ne da samar da tan din Shinkafa dubu Takwas (8000) a rana an kafa kamfanin ne a shekarar 2015.
” A yau mun samu ci gaban samar da tan na Shinkafa dubu dari biyar (500,000) a rana daya ta hanyar yin amfani da na’u’orin zamani da kuma fasahar zamani.
” sababbin kayayyakin na zamani suna taimakawa wajen samar da gudanar da ayyuka cikin Sauri da kuma yin aikin da yawa , kuma a halin yanzu muna samun Shinkafar da ake sarrafa wa a cikin sauki a kusa da mu ba kamar a can baya ba sai an yi tafiyayya zuwa wurare masu nisa kafin a same ta domin sarrafa ta zama abincin da kowa zai yi amfani da shi, aci a koshi,duk wannan kokari ne irin na shawarwarin da ka bayar a matsayin Uba”, ya gaya wa Sanatan.
Sai kuma ya ce kamfanin a halin yanzu na da ingantaccen iri mai kyau da zai iya samar da tan dubu Goma sha biyu 12,000 kuma ya ce kamfanin na da hadin Gwiwa Gwiwa wadansu hukumomin Gwamnatin tarayya domin tabbatar da samar da Shinkafa lafiyayya kuma mai tsafta tare da inganci domin amfanin al’umma baki daya.
Alhaji Jodi ya kuma yi bayani a game da matsalar kayan da suke sarrafa wa da kuma tsadar sufuri da sauransu a matsayin wadansu kalubalen da ake fuskanta abin da ya bayyana masu neman saukin gaggawa daga Gwamnati kuma a kowane irin mataki
Ya kuma yi amfani da wannan ziyarar da Sanata Wamakko ya kai inda Alhaji Jodi, ya zagaya da Sanatan domin ganin irin kayan da ake amfani da su da kuma yadda Sule aiwatar da ayyukan na su, Sanata Wamakko ya yi kira gare shi da sauran shugabannin kamfani da su ci gaba da aiwatar da ayyukan da suke yi a koda yaushe domin ci gaban kasa.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.