Home / Ilimi / Sanata Wamakko Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Miliyan 317 Ga Marayu

Sanata Wamakko Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Miliyan 317 Ga Marayu

Daga  Abdullahi Dan garin nan
Shugaban kwamitin harkokin tsaro kuma mataimakin shugaban kwamitin yaki da cin hanci sanata Aliyu Magatakayrda Wamakko, yq kaddamar da Rabon tallafin marayu na naira miliyan 317.7 domin rabawa marayu 1,176 karkashin kungiyar bayar da tallafin musulunci ta (Islamic Relief Organization)
 Wadanda suka amfana sun hadar da maza da mata, da sula fito daga kananan hukumomi 23 na Jihar Sakkwato.
Da yake jawabi a wajen taron Sanata Wamakko, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar sanatocin arewacin tarayyar Nijeriya, ya ce an fara wannan shirin ne da tantance marayu a shekarar 2009.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da mai taimakawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Bashir Rabe Mani Dan masanin mani ya Sanya wa hannu.
Wamakko wanda ya samu wakilcin tsohon ministan harkokin sufuri Alhaji Yusuf Suleiman, sanata Wamakko wanda ke wakiltar mazabar Sakkwato ta Arewa, ya kara da cewa ” wannan kungiyar sananniya ce da ta dade tana irin wannan aikin da kuma yin aikace aikace gine gine a cikin Jihar.
“Ayyukan sun hada da gina makarantun Islamiyya, gina masallaci da kuma bayar da taimako ga mabukata ta fuskoki daban daban”.
” Don haka ne kungiyar taso domin bayar da tallafin yin karatu ga wadannan marayu wanda zai taimakawa marayun su ci gaba da karatunsu a fannonin da suka zaba”.
“Wannan an yi shi ne domin suma su samu ilimi, wanda hakan zai ba su damar dogaro da kansu ta yadda za su amfani al’umma”.
Sanata Wamakko ya kuma yi kira ga masu kula da marayun da suka amfana da su ji tsoron Allah ta fuskar yin amfani da abin da aka ba su kamar yadda ya dace, ma ana dai suyi amfani da shi kamar yadda aka tsara.
Ya kuma kara fadakar wa kamar haka ” ku tuna fa zamu yi bayanin dukkan abin da muka aikata a ranar gobe kiyama”.
Ya kuma yi kira ga daukacin al’umma baki daya da su yi amfani da dukkan abin da suke da shi wajen taimakawa marayu, Zawarawa da masu karamin karfin da ke cikin al’umma.
“Domin babu wani abin da mutum zai bayar da ke da kankanta ko kuma yawa, indai za a ba marasa a cikin jama’a domin Allah”.
Sanata Wamakko ya kuma yi jinjina ga kungiyar da ke kasar Saudiyya bisa irin abubuwan da suke yi wa jama’a na aikace aikace aikace aikace a Jihar Sakkwato.
Ya kuma yi kira ga kungiyar da kada ta gajiya wajen irin ayyukan da suke gudanarwa musamman irin yadda ya kara rokon su da su kara yi wa Jihar Sakkwato wadansu ayyukan.
A ta bakin wakilin kungiyar Huzaifa Tahir cewa ya yi wannan tallafin na shekarun 2011,2012 da shekarar 2013 ne.
Kamar yadda ya bayyana cewa na shekarar 2014, za a Rana shi a nan gaba kadan.
Bako mai jawabi sheikh Yahuza Shehu Tambuwal Limamin masallacin Juma’a na Uthman bin Affan Sakkwato kira ya yi ga daukacin jama’a da su taimakawa marayu kamar yadda aka bukaci kowa a cikin musulunci.
Dukkan wadanda suka yi jawabi a wurin taron sun yi godiya fa Sanata Wamakko da ya kawo wannan kungiya Jihar Sakkwato a lokacin da yake Gwamnan Jihar, sun kuma Jinjinawa kungiyar bisa abin da take aiwatarwa.
Da yake magana a madadin wadanda sula amfana Ahmad Umar da Safiya Babuga, sun godewa Sanata Wamakko da kuma kungiyar bisa abin da suka yi wanda hakika zai kara bunkasa harkar iliminsu baki daya.
Sun kuma yi alkawarin yin amfani da kudin kamar yadda aka bayar domin yi.
An dai bayar da mafi karamin kudi ga wadanda suka amfana na naira dubu 200,000 mafi yawa kuma naira dubu 400,000.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.