Home / Kasuwanci / Yan Majalisar Dattawa Sun Tattauna Yadda Za a Farfado Da Masana’antu – Uba Sani

Yan Majalisar Dattawa Sun Tattauna Yadda Za a Farfado Da Masana’antu – Uba Sani

Imrana Abdullahi
Ssnatan da ke wakiltar yankin kaduna ta tsakiya sanata Uba Sani ya bayyana cewa sun tattauna da wadansu wakilan kungiyar masu masana’antu da suka kai masu ziyara a ofishin shugaban majalisar Dattawa Alhaji Ahmed Lawan.
Sanata Uba Sani ya ci gaba da bayanin cewa sun dai tattauna a lokacin taron irin yadda za a hada hannu tsakanin majalisar da kungiyar masu masana’antu ta kasa domin a samu ci gaban da kowa ke bukata.
Za dai a iya cewa wannan yunkuri zai farantawa yan Nijeriya rai ganin irin yadda tsawon shekaru masana’antu a kasar suka durkushe ga kuma dimbin matasa maza da mata na gararambar neman aiki.

About andiya

Check Also

TINUBU YA NADA GEORGE AKUME A MATSAYIN SAKATAREN GWAMNATIN TARAYYA

Daga Imrana Abdullahi Kamar dai yadda jaridar “Vanguard” ta rawaito cewa tun bayan rantsar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.