Daga Imrana Abdullahi
Akwai jita-jita cewa tsohon gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar, APC.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun nuna cewa Barista Shema ya ziyarci shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a ranar Asabar.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance game da ziyarar, hasashe ya nuna cewa matakin na baya-bayan nan na iya zama matakin karshe na kammala shirin ficewa daga PDP Shema zuwa APC mai mulki a Jiharsa ta Katsina da kasa baki daya.
Duk dai abin da zai kasance lokaci ne zai tabbatar da hakan.