Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Dayyabu Mai Gwanjo,ya bayyana gamsuwa da irin Canjin da aka samu a cikin jam’iyyar APC a matsayin muhimmin al’amarin da ya faru a cikin jam’iyyar APC a jihar Kaduna.
Dayyabu Mai Gwanjo ya bayyana hakan ne a lokacin da suka halarci babban ofishin jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, inda ya ce daga zuwansu harabar ofishin na Jiha sun ga komai ya canza, fuskokin sun canza kuma yanayin abubuwan da ake gudanarwa duk sun canza da kuma irin yadda aka karbi tawagar neman jam’iyyar ta tsayar da Kwamared Shettima Yarima dan takara, ya bayyana gamsuwa da irin karbar da aka yi masu.
“Muna yi wa shugabannin jam’iyya godiya da irin yadda kuka nuna cewa ku lallai shugabanni ne na jam’iyya.
Alhaji Dayyabu Mai Gwanjo ya kara da cewa babban dalilin zuwansu ofishin jam’iyya na jiha shi ne domin mu kawo dan takarar danku mai neman jam’iyya ta tsayar da shi takarar neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya mai kokari da aiki tukuru da ke da dimbin alkairi da yawa, mu da muke da yawan shekaru min san wannan bawan Allah bashi da aikin da ya wuce taimakon al’umma kullum duk inda ake neman taimako ya na wurin duk inda za a yi wata hidima da an gayyace shi aguje zai je inda aka gayyace shi, kun ga irin wannan shi ne dan sakon da za a tura a samu abin da ake bukata don haka muke son a ba wannan bawan Allah amanar Kaduna ta tsakiya in Allah yaso ba za mu yi da na sani ba, aba wanda ya san aikinsa domin ba zai bayar da kunya ba.

“Abin da ya sa jam’iyyar APC ita ce duk Afirka babu irin ta kuma a Najeriya babu jiha kamar jihar Kaduna domin hedkwatar tarayyar Najeriya daban Abuja Legas duk da ban, amma arewacin Najeriya ita ce Najeriya kuma Arewacin Najeriya Kaduna ita ce hedkwatar kuma hedkwatar Kaduna ita ce Kaduna ta tsakiya don haka don Allah don Annabi jam’iyyar APC a zo wanda zai wakilci Kaduna ta tsakiya, kuma muna gaya wa duniya cewa Kwamared Shettima Yerima zai iya wannan aikin.Muna jin dadi da irin yadda jam’iyyar APC ta bayar da damar a Gwada Kwanji ayi zabe sosai a dauko dan takarar da jama’a suke so, muna godiya mun gode mun gode kwarai.
THESHIELD Garkuwa