Home / Uncategorized / Shugaban Majalisa Abbas Tajuddeen Ya Samar Da Manyan Makarantun Gwamnatin Tarayya Guda Hudu A Zariya

Shugaban Majalisa Abbas Tajuddeen Ya Samar Da Manyan Makarantun Gwamnatin Tarayya Guda Hudu A Zariya

Manyan makarantun za su lashe kudi biliyan 80, inji Abbas Tajuddeen
An bayyana cewa aikin samar da manyan makarantun na Gwamnatin tarayya a garin Zariya zai lashe makudan kudi naira biliyan 80
Ayyukan dai sun hada da Kwalejin Koyar da aikin jinya da Unguwar Zoma ta Gwamnatin tarayya,da za a gina ta da nufin rage matsalar da ake fama da ita wajen kula da harkokin lafiya a Jihar Kaduna.
Sauran makarantun sun hada da makarantar kwalejin Ilimi ta Gwamnatin tarayya, Jami’ar yin karatu daga gida da kuma kwalejin koyon aikin shari’a.
Dokta Abbas Tajuddeen, shugaban majalisar wakilai cewa ya yi aikin dai na da tsawon watanni 18 ne a kammala aikin kuma za su lashe makudan kudi har naira biliyan 80.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da fara gudanar da ayyukan da aka yi a ranar Lahadi a garin Zariya.
Kamar yadda shugaban majalisar ya bayyana cewa an samar da wadannan manyan makarantu na Gwamnatin tarayya ne bayan an dade ana kaiwa da dawowa, saboda kwalejin koyon aikin jinya da unguwar Zoma zai taimaka kwarai wajen rage matsalar karancin masu irin wannan aikin a Jihar kaduna, arewaci da kasa baki daya.
Sai ya kara da cewa ita kuma.makarantar koyon ayyukan shari’a za ta taimaka kwarai wajen kara zurfafa harkokin bincike a bangaren shari’a da kumankwalejin ilimi ta Gwamnatin tarayya za ta samar da malaman makarantar da ake bukata ga Jihar Kaduna da Najeriya baki daya.
Kamar yadda ya ce jami’ar yin karatu daga gida zai ba ma’aikata tare da sauran jama’a damar ci gaba da karatunsu.
Sai shugaban majalisar ya kara fayyace cewa suna kara yin godiya tare da jinjina ga Gwamnatin jihar Kaduna da ta samar da wurin aiwatar da wannan ayyukan.

About andiya

Check Also

Senator (Barr) Sunday Marshall Katung decries Abduction Of 22 Women And Children

As a result result of too much security challenges in some local Governments in Kaduna …

Leave a Reply

Your email address will not be published.