Related Articles
Daga Imrana Abdullahi Kaduna
Da Dumi duminsa: labarin da muke samu a yanzu na bayanin cewa shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna Alhaji Aminu Abdullahi Shagali ya sauka saga mukaminsa na shugaban majalisar.
Kamar yadda muka ga takardar ajiye aikin da ya rubuta da hannunsa ya kuma Sanya mata hannu daga karshe Lamar yadda ka’idar rubuta irin wannan takarda ta tanadar cewa ya ajiye aikin ne domin kashin kansa.
A labarin da muke samu yanzun nan na cewa honarabul Yusuf Ibrahim Zailani ne ya zama sabon shugaban majalisar dokokin ta kaduna.
Kuma honarabul Muktar Isa Hazo ne sabon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar kaduna.