Home / Labarai / Shugabannin Arewa Ne Matsalar Yankin – Gwamna Matawalle

Shugabannin Arewa Ne Matsalar Yankin – Gwamna Matawalle

Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad  Bello Matawalle, ya bayyana a fili a wajen wani babban taron Shekara shekara na kungiyar marubuta a kafofin yada labarai mai su na ( Arewa Media Writers) da aka yi a garin Kaduna cewa shugabannin arewa ke da alhakin matsalar tsaron da ya mamaye yankin da ya kasance mafi yawa da kuma yawan al’umma Najeriya.
Muhammadu Bello Matawalle ya yi wannan hangen ne yayin da yake gabatar da wata takarda mai taken “Yaki da yan bindiga a yankin arewa maso yamma: Ƙalubale da hanyar warware su” a wurin taron ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar marubutan Arewa “Arewa Media Writers” a Kaduna.
Ya ci gaba da fayyace bayanin da cewa  shugabannin Arewa suke da alhakin yanayin da yankin ke ciki, wanda ya haɗa da aikata manyan laifuka kamar fyaɗe, kisan mata da ƙananan yara, sace mutane, fashi da makami da sauran manyan laifukan da suka mamaye yankin.
A cewar gwamnan, arewa ta rasa kyakkyawan shugabancin da zai jagoranci gina yankin da magance matsalolinsa.
Ya kuma ƙara da cewa manyan masu faɗa a ji na yankin arewa ba su da wani kudiri face su samu damar ɗarewa kan mulkin siyasa.
Matsalar Da Zamfara Ke Ciki, Bello Matawalle ya kara da cewa lokacin da ya amshi mulki a 29 ga watan Mayu 2019, Zamfara ta riga ta shiga halin ƙaƙanika yi na rashin tsaro da ya shafe lokaci mai tsawo.
Gwamnan ya ce jihar bata da wani labari a kullum sai na zubar da jini, wuta, sace-sace da kuma korar mutane daga mahallinsu musamman waɗanda ke rayuwa a yankunan karkarar Jihar.
Gwamna Matawalle, wanda kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara, ya wakilta, ya ce:
; “Rikicin ya kawo karuwar talakawa da kuma rashin abinci, Zamfara ta kama hanyar rugujewa ta kowane ɓangare saboda tada zaune tsaye a yankunan karkarar mu da ma Arewa baki ɗaya.”
“Ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi sun zama gidan aikata ta’addancin yan bindiga duk da cewa an daina haƙar ma’adanai a yankunan”, inji shi
Arewa Ta rasa Masu Tallafawa
Gwamnan ya koka kan rashin masu taimakawa daga ɓangarorin yan siyasa, waɗanda ke amfani da wannan damar wajen cimma wani kudirinsu na siyasa.
“Dukkan mu mun ga irin yadda manyan kudu maso gabas da kudu maso yamma suka ɗauki mataki cikin haɗin kai a kan duk abin da ya taso a yankinsu.” inji wakilin Gwamnan.
“Munga yadda suke da manufa ɗaya kuma ba su gajiyawa wajen kokarin kawo ci gaba a yankinsu”.
Gwamna Matawalle ya yi kira ga manyan shugabannin yankin arewa da su farka daga baccin da suke, su haɗa kansu domin fuskantar duk wani ƙalubale.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka A Bakura Da Maradun

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.