Home / News / Tafiyar Kwankwaso Harka Ce Ta Son Zuciya – Ganduje

Tafiyar Kwankwaso Harka Ce Ta Son Zuciya – Ganduje

Tafiyar Kwankwaso Harka Ce Ta Son Zuciya – Ganduje

 

Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana tafiyar Kwankwaso da su Dakta Rabi’u Suleiman Bichi ya baro da cewa harka ce ta son zuciya da bai dace kowa ya amince da ita ba.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar wadanda suka dawo APC karkashin shugaban PDP na Jihar Kano Rabi’u Suleiman Bichi a wani taron da aka yi a gidan Gwamnatin Jihar

Gwanduje ya tabbatar masu cewa “Kun dawo gida daman can gidan ku ne Marhaba, lale da  jabbama da kuma amince da wannan tafiya”.

Na san halin Kwankwaso Kwankwaso abin da ya yi na sani in ya yi Dariya ko yake na sani domin zamantare da Juna.
A shekarar 1999 ba kwankwaso ya ci zaben fitar da Gwanin zama dan takarar Gwamna a PDP ba, saboda ko a karamar hukumar Gabasawa mun san abin da aka yi kuma wadanda suka yi duk suna nan muna tare da su, don haka ko shekarar 1999 ba shi ya bani mataimakin Gwamna ba
“Mundange sai an sake zabe domin bamu amince ba amma jami’an da suka zo daga Abuja domin yin zaben fitar da dan takarar Gwamnan PDP a Kano sai suka ce don Allah ko an sake zaben shima zai ce bai amince ba
Don haka Ganduje ka yi mataimaki kuma na amince har muka gama mulki ba rigima ba komai aka kammala mulkin lafiya
“Atiku yana mataimakin shugaban kasa amma ya raina shi”, inji Gwamna Ganduje.
“Kwankwaso mai sa a ne ba dabara ba a siyasa, bayan mun fadi zabe a kano aka bashi minista, ya ce in yi masa SA, ni kuma na ce a’a”, duk inji Gwamna Ganduje
“Na kwana biyu ban yi bacci ba, dalili shi ne farin ciki ya hana ni bacci ba, na biyu kuma bakin ciki ya hana ni bacci. Dalili kuma shi ne da maga an kai Kwankwaso wurin Buhari ba tare da an yi shawara da ni ba, na ce hana wannan mutum zai yi mini, sai kuma ranar da Naga cewa Kwankwaso ya fita daga APC rannan ma ban yi bacci ba saboda farin ciki duk abin da Kwankwaso keyi saboda kansa ne”.
Babbar matsalar Kwankwaso baya son jin shawara shi ya Fi kowa iyawa, ko mai gadinka,ko yaron gidanka koma direbanka sai ya zamo basirarsa ta fi taka duk hana Allah ke hukuncinsa.
Yana ta cewa za a dage kafar wando tun kafin ayi zabe, to shi bai san dan Fulani ba daman kafar wandonsa a dage take.
Ya ci gaba da cewa zai iya kwana yana bayar da labarin aika aika, muna son wadanda suka gaje mu suyi abin kirki
Ga wadanda suka dawo APC daga PDP Gwamna Ganduje ya ce masu za a yi tafiya tare ba nuna wani bakinciki ko bambanci a tsakanin mu komai za ayi tare.
 Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas, cewa ya yi duk mai mutunci ba zai iya bin wancan tsarin ba.
Wadansu sun dauka Kano kayan Kwankwaso ne mu kuma muka ce  a a kano kayan mu ne ta dukkan ganawa ce.
An dai saka wa Dakta Rabi’u Suleiman Bichi wata sabuwar hula shaidar ya shiga sabuwar tafiya.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.