Home / Labarai / Jihar Zamfara Na Da Yayan Bedin Da Ya Fi Na Kowace Jiha Kyau – Zailani Baffa

Jihar Zamfara Na Da Yayan Bedin Da Ya Fi Na Kowace Jiha Kyau – Zailani Baffa

Mustapha Imrana Abdullahi
An bayyana Jihar Zamfara a matsayin jihad da ke da yayan Bedin da ya ci na kowace Jihar kyau a fadin Nijeriya.
Zailani Baffa mai taimakawa Gwamnan Jihar Zamfara ne a kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta Liberty a kaduna
Zailani Baffa ya ce wannan arziki na yayan Bedi kamfanoni da yawa na bukatar shi domin sarrafa wa ayi abubuwa da dama na inganta rayuwar jama’a.
Baffa ya kuma ci gaba da cewa kamfanonin sarrafa ma’adinai da dama ne da ke kasar Sin wato Chaina sula gayyaci Gwamnan Zamfara Alhaji Mihammadu Bello Matawallen Maradun saboda zaman lafiya da aka samu a Jihar.
“Akwai ma’adinai guda 17 a dankare a cikin Jihar Zamfara cikinsu had da Gwal kuma kamfanonin suna bukatar su domin amfanin sunita baki daya.
Ana nan za a samar da wata ma’aikatar da za ta yi aiki a kan kiyaye hakkin dukkan mai hakki idan wani kamfanin ma adanai na bukatar hakowa da sarrafa ma’adanin Jihar Zamfara, tun daga kan karamar hukuma zuwa jama’ar da ke cikin ta baki daya.
“Akwai wata kasuwa a kasar Dubai da na gani a tashar Talbijin ta channels da ake cewa kasuwar Zamfara Gwal, kawi ana sayar da Gwal na Jihar Zamfara haka kawai ba tsari, shi yasa yanzu Gwamnan Zamfara ya samar da ingantattun tsare tsaren da kowa ne dan Jihar Zamfara zai amfana da arzikin da Allah ya horewa Jihar”, inji Zailani Baffa.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.