Home / Labarai / Za Share Dukkan Yan Ta’adda Baki Daya – Masari

Za Share Dukkan Yan Ta’adda Baki Daya – Masari

 Imrana Abdullahi
Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa al’ummomin kananan hukumomi takwas da suke iyaka da Dajin rugu suna cikin halin zaman dar-dar, zullumi da rashin tabbas sakamakon yadda ‘yan ta’adda suke kai masu hare-hare da manyan bindigogi wanda ke zama sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau a yayin da ya amshi bakuncin Babban Hafsan Sojojin Kasa na kasar nan Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai wanda ya kawo mashi ziyarar ban girma a Fadar Gwamnati dake nan Katsina.
Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa alamu na nuna an dan fara samun sauki, amma akwai bukatar hukumomi su kara wa jami’an tsaro damara ta yadda za su fuskanci wannan aiki na kakkabe wadannan ‘yan ta’adda, ta fuskar kara yawan su da kuma kayan aikin.
Ya kuma kara da cewa wajibi ne ayi amfani da karfin Soja na gaske domin wadanda ake yakar nan kwakwalwar su ta toshe, ba su fahimtar wani abu idan ba karfin makamai ba wanda kuma shi ne hanya daya tilo da ta rage da za abi wajen fatattakar su domin a sami zaman lafiya a wadannan yankuna dama kasa baki daya.
Gwamna Masari ya kuma yi nuni da cewa dole sai an yi ma wannan yaki salon ‘a kashe Maciji kuma sare kan shi’, domin idan har ba haka aka yi ba to nan gaba suna iya sake waiwayowa da shirin daukar fansa.
 Ya ja hankalin hukumomin tsaro kan bukatar dake akwai ta gaggauta kammala wannan yaki da ‘yan ta’adda domin kauce wa sa hannu ko katsalandan daga wajen kasar nan.
Tun farko a nashi jawabin, Laftanar Janar Tukur Buratai ya shaida wa Gwamna Aminu Bello Masari cewa ya zo Katsina ziyarar aiki domin duba yanayin da ayyukan Soja suke tafiya a karkashin runduna ta 17 ta sojan kasa da ke  Katsina.
Ya kuma jaddada cewa aikin kakkabe bata gari, musamman ‘yan ta’adda shi suka sa a gaba a duk sassan kasar nan.
Laftanar Janar Buratai ya kuma shaida wa Gwamnan cewa domin nuna muhimmancin da suka ba matsalolin da suka addabi wannan yanki, rundunar Sojojin ta dauko bukin ranar Sojoji na shekara shekara da take yi daga jihar Filato zuwa Katsina kuma a garin Faskari wato a dajin Faskari za ayi bikin rawar Dajin na Bana.
Sun yi hakanne domin su sami damar shiga tare da tsefe wannan daji baki dayan shi tare da tabbatar da ba a bar ma ‘yan ta’adda damar zama cikin shi ba ballantana su mike kafa har su addabi mutane.
A madadin rundunar Sojin, Laftanar Janar Buratai ya gayyaci Gwamna Aminu Bello Masari domin ya halarci wannan buki da za su yi a matsayin Babban Bako na Musamman.
Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu, Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da sauran manyan jami’an Gwamnatin Jiha suka halarci wannan zama wanda ya hada da Birgediya Janar Aminu Bande Babban hafsan runduna ta 8 ta Sojin Najeriya da ke Sokoto.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.