Home / Labarai / Tsaro: Sakkwatawa Da Zamfarawa Sun Jinjinawa Gwamna Bello Matawalle

Tsaro: Sakkwatawa Da Zamfarawa Sun Jinjinawa Gwamna Bello Matawalle

 Al’ummar Jahar Sokoto da Zamfara sun  bayyana farin cikinsu da matakan sojan da  a ka dauka a gabashin Sokoto,.
Sun bayyana farin cikin ne tare da yin jinjina mai yawa ga Gwamna Bello Mutawalle na Jihar  Zamfara a kan zuwan sa kasar Nijar don neman hadin kan jami’an tsaro kasar na ganin an samu nasara a yaki da yan ta’adda da Sojojin Nijeriya suke aiwatarwa.
 Al’ummar Gabashin Sokoto sun yaba da wannan kokari tare da neman Gwamnatin tarayya ta baiwa wannan Shirin dukkan goyon baya da ya dace domin a cimma nasara.
 Sai kuma irin namijin kokarin Gwamnan Jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal na fitowa fili ya gaya ma Shugaban kasa gaskiya a kan yanayi da halin da al’umma take ciki.
 Jama’a suna ta’allaka samun nasara ga matakin gaggawa da Gwamnatin Nijar ta dauka na dakile dukkan hanyoyin da yan ta’adda za su yi amfani da su don tsira daga farmakin Sojin  Najeriya a gabashin Sokoto.
Sakamakon wannan kokarin ne a halin yanzu ake ci gaba da samun rahotannin  nasara bisa  Yaki  da ayyukan ta’addanci da Sojojin Najeriya tare da sauran jami’an tsaro a yankin gabashin jahar Sokoto da wani bangare na jihohin Katsina da Zamfara suke yi.
Wannan dalilan samun nasara bai rasa nasaba da ziyara da Gwamnan jahar Zamfara, Honarabul  Bello Muhammad Mutawalle ya kai ga Shugaban Kasar  Nijar,  Mohamed Bazoum   don neman agaji da gudumuwar kasar Nijar a kan ta toshe hanyoyin da yan ta’adda da ake kaiwa farmaki ke amfani da su wajen tserewa zuwa kasar, inji Malam Usman Tozai.
Bayanin da wasu magidanta a Tozai da Katanga da ke gabashin Sokoto da aka zanta da su da wasu jama’a a garuruwan Isa da Sabon Birni sun tabbatar da cewar, al’ummar yankin sun yi matukar godiya ga matakin soja da Gwamnan Sokoto ya roki Shugaban Kasa, mussaman ma abin da ya kara tabbatar da nasara shi ne sakamakon ziyara da Gwamnan jahar Zamfara ya kai a Nijar don samun taimakon Sojojin kasar,.
“Don kuwa an ga manyan motoci na sojojin Nijar a kan iyakar  Madawa a Sabon Birni da wasu garuruwan na Burku-suma na kan iyaka ana hana yan ta’adda shiga Nijar”, inji majiyar mu.
Haka ma Sojojin Nijar sun datse hanyoyin daji da yan ta’adda ke amfani dasu inda suka hallaka fiye da yan Ta’adda dari  200 da ke gudun tsira daga hare haren Sojojin Najeriya.
Baya ga wannan ma Sojojin Nijar tare da na Najeriya suna rangadi da motoci yaki don ganin ba a bar wani dan ta’adda ya samu kafar shiga ba.
A makon jiya dai gwamnan Jahar Zamfara Honarabul  Bello Muhammad Mutawalle ya ziyarci Shugaban Kasar  Nijar, Mohamed Bazoum   don ganawa da shi a kan yadda zai taimaka ga jami’an tsaro kasar su rinka killace hanyoyin shiga kasar daga kan iyaka da yankin jahar Zamfara, sakamakon bayanan da ake samu na yan ta’adda suna kai hare haren ta’addanci a wasu garuruwan da ke kusa da kan iyaka kuma suna samun mafaka a cikin Nijar.
Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum   wanda ya yaba ma Gwamnan Zamfara a kan wannan namijin kokari na zuwa da kansa don neman mafita ga al’ummarsa, sai ya  bayar da umurnin Sojoji da sauran jami’an tsaro kasar da su tabbatar da sun dakile dukkan hanyoyin da yan ta’adda ke amfani dasu su na shiga Nijeriya ko kuma neman mafaka.
Hakan ya yi amfani jim kadan bayan tawagar shugaban kasa ta kawo ziyara Sokoto don yin jaje a ka ga Sojoji sun fantsama Dajin Sabon Birni da na Isa da  Gundumi suna farautar yan ta’adda, mussaman shugabansu Bello Turji da yaran sa da ke addabar al’umma a gabashin jahar Sokoto a garuruwan Tozai, Adama Satiru, Katanga, Bafarawa, Gebe da gabashin Shinkafi a Jahar Zamfara da ke arewa maso Yammacin Najeriya.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.