Home / Kasashen Waje / Tsohon Shugaban Kasar Nijar Tandja Mamadou Ya Rasu

Tsohon Shugaban Kasar Nijar Tandja Mamadou Ya Rasu

Imrana Abdullahi

A cikin wata sanarwa ce da aka karanta a kafar talabijin ta gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana rasuwar tsohon shugaban kasar malam Tandja Mamadou.

Tuni dai gwamnatin kasar karkashin jagorancin shugaban Issoufou Mahamadou ta mika sakon ta’aziyarta ga ‘yan kasar da iyalan tsohon shugaban kasar tare da ayyana kwanaki uku na zaman makoki.

Malan Tandja Mamadou dai ya jagorancin kasar jamhuriyar Nijar din ne na tsawon shekaru goma (10) daga shekarar 1999 zuwa Watan Febarairun 2010 lokacin da sojojin kasar suka yi mishi juyin mulki biyo bayan kwaskware kundin tsarin mulkin kasar domin samun damar ci gaba da mulki.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.