…Mun Gyara Magunan Ruwa – Dokta Haire
Hadiza Badamasi, babbar jami’a ce da ke aikin ganin an samu nasarar kiyaye muhalli ta hanyar kulawa da itatuwa musamman a cikin birane wato Urban tree revival initiative (UTRI), da ta yi wani taron gangamin al’umma Maza da Mata da suka zagaya cikin garin Kaduna da nufin wayar wa da jama’a kai game da muhimmancin itatuwa a cikin birane domin kula da muhalli.
Hadiza Badamasi ta shaidawa manema labarai a Kaduna cewa sun shirya taron gangamin jama’a ne da aka zagaya cikin birnin Kaduna a kan tituna da suka hada har da matattarar jama’ar babbar Kasuwar Kaduna wato (central Market) da nufin kowa ya fadaka a kan ayyukansu.
” Babban dalilin yin wannan gangami na jama’a shi ne domin fadakar da kowa game da batun sauyin yanayi da kuma illolinsa ga rayuwar zamantakewar dan Adam.Kuma wannan gangamin da muka yi zai taimakawa dimbin jama’a domin kowa ya isha cikin aikin kula da ingantawa da kare muhalli daga dukkan wasu illolin da ke yin barazana ga muhallin da ake da shi a cikin jama’a”.
Hadiza ta kara da cewa ” hakan kuma zai taimakawa wa hatta Gwamnati a matsayinta na hukuma ta ci gaba da kara kaimin yin abin da ya dace, haka kuma da hukumomi da dai daikun mutane duk za su ci gaba da fadaka a kan batun canjin yanayi da ke shafar muhalli da hakan zai taimaka kwarai wajen rungumar tsare – tsare da dukkan tanaje tanajen dokokin kula da canjin yanayi”, kamar yadda Hadiza ta tabbatarwa manema labarai.
Mun Yi Kokarin Gyara Magudanan Ruwa
Da yake tofa albarkacin bakinsa lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a wajen taron gangamin babban jami’in Dokta Umar Haire babban jami’in kula da al’amuran da suka shafi Shara da abubuwan da ake zubarwa na hukumar da ke kula da babban birnin Kaduna wato ( Kaduna capital territory Authourity).
kira ya yi ga daukacin al’umma da su tabbatar sun ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga dukkan manufofin da abubuwan da Gwannati ta fito da su saboda dukkan abin da Gwamnatin ke yi domin jama’a ne take yin su, don haka a rungumi tsare tsaren Gwannati a kuma yi abin da ya dace muna tabbatar wa da jama’a cewa na ganin babu wata al’ummar da ta samu kanta a cikin matsalar ambaliyar ruwa a koda yaushe.
“Mun yi dukkan abin da ya dace muga cewa an gyara magudanan ruwa mun kuma cire duk wani abin da ba a so wanda hakan ya bayar da damar aka samu nasarar bude hanyoyin ruwa sosai, idan aka je Kogin Kaduna za a ga cewa Gwannati ta yashe shi sumul”.
Saboda haka ne ma wadansu Jihohin ke yin koyi da abin da Jihar Kaduna ta ke yi na Gyare gyaren magudanun ruwa saboda irin kokari wajen yashe manyan magidanan ruwa da Jihar ta yi”.
Saboda Gwamnatin ta zuba makudan kudi domin ganin an yashe Kogin Kaduna wanda sakamakon hakan ruwa na wuce wa ta wurin kamar yadda ake bukata ba tare da samun wata matsala ba.
“Da wannan irin Namijin kokarin ne da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi muke saran cewa babu abin da zai faru na wata matsalar da hukumar kula da hasashen yanayi ta ( NIMet) ke hasashen zai faru cewa za a iya samun ambaliyar ruwa, saboda haka ne mu muke bayanin cewa da irin yadda Gwamnatin ta yi kokari hakika wannan zai zama sai dai tarihi kawai, kuma a dalilin hakan ne muke yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su hada hannu da mu wato Gwamnatin Jihar Kaduna domin ganin hakan da wasu ke hasashe bai faru ba a dukkan al’ummar mu baki daya.
” Domin bukatun mu shi ne garin Kaduna dai na mu ne saboda haka muke yin kira ga dukkan jama’a su Sani fa garin Kaduna birnin mu ne don haka ya dace mu yi dukkan mai yuwuwa muga mun kare birnin na mu ta yadda zamu samu kyakkyawa kuma ingantacciyar rayuwa, hakika a kokarin samun hakan ana bukatar kowa ya Sanya hannunsa da nufin bayar da gudunmawa.
Dokta Umar Haire Mai kula da batun harkokin shara na hukumar babban birnin Kaduna wato ( incharge of west managemant of Kaduna Capital territory Authourity)
An dai samu halartar jami’an da ke kula da Gandun Daji domin kiyaye masu barnata bishiyoyi daga ma’aikatar Gona ta Jihar Kaduna da dai sauran masana muhalli duk sun halarci gangamin.