Home / MUKALA / Walimar Cika Shekaru Biyu Da Auren Injiniya Kailani, Khadija Ta Yi Armashi

Walimar Cika Shekaru Biyu Da Auren Injiniya Kailani, Khadija Ta Yi Armashi

Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda karantarwar addinin Islama ta bayyana cewa aure sunnah ce ta Manzon tsira Annabi Muhammadu (S.A.W) da ya umarci al’ummarsa da su yi aure domin su hayayyafa saboda ya yi alfahari da al’ummar a ranar Gobe idan alkiyama ta tsaya.
A kokarin ganin an raya sunnar Manzon tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da kuma sahabbansa baki daya.
A ranar Talatar da ta gabata ne da ta kasance ranar Babbar Sallah, Injiniya Kailani Muhammad da amaryarsa Khadija Bashir Mashi, suka tara dimbin jama’a domin yin walimar murnar Aurensu da suka cika shekaru biyu da yinsa.
A wajen taron dai jama’a da dama sun gabatar da jawabai game da nagarta da kuma kyawawan halayen Injiniya Dokta Kailani Muhammad irin yadda yake taimako da Kaunar ci gaban al’umma da suka hada da yin maraba da jama’a yaro da babba.
A wajen taron an yi murna kwarai da Allah ya albarkaci auren da ya yi tsawon shekaru biyu da samun yaro mai suna Muhammad Bashir Ishraq Kailani Muhammad, sai Fatan Allah ya raya shi tare da dukkan daukacin yayan Injiniya Kailani Muhammad da suka kasance Maza da Mata.
Malam Muhammad na daya daga cikin mutanen da suka gabatar da jawabi ga jama’a a kan halaye da irin yadda Injiniya Kailani Muhammad ya dauki hidimar jama’a matsayin abin yinsa dare da rana domin ganin rayuwar al’umma ta inganta.
Ga dai irin abin da Malam Muhammad ya gayawa jama’a, ni a iya Sani na a koda yaushe na hadu da Injiniya Dokta Kailani Muhammad na san shi da yin kyauta ga kowa kuma ya na kokarin ya mika wa mutum  ba tare da wani ma ya san ya yi wa wani ko wasu kyauta ba.
Kuma duk lokacin da ka gan shi zaka gansa ya na kokari da jama’a ta fannin rayuwarsu, a cikin kokarinsa ne ma ya sa har ya samowa jama’ar unguwar sabuwar Rigasa ta bangaren layin Abuja aikin canza turken fal wayar wutar lantarki na tsawon milimita daya da za a Sanya manya kuma turakun lantarki na kankare domin amfanin dimbin jama’a, wanda kamar yadda Malam Muhammad ya bayyana cewa idan za a samu mutane da yawa da Allah ya wadata su, su rika kokarin kawo ci gaba da hakika lamarin ya yi kyau.
Sai kuma Malama Sa’adiyya da ta kasance kawa ga Mahaifiyar Khadija Bashir Mashi, da ta yi jawabi a game da irin halayyar kawar wato matar Injiniya Dokra Kailani Muhammad, cewa ta yi ta na murna tare da farin cikin yadda Allah ya Sanya aka samu kaiwa har tsawon shekaru biyu da yin wannan aure da Allah ya albarkace shi da samun Muhammad Bashir Israk.
Hakika kawa ta Khadija mace ce mai hakuri da ta kasance mai son jama’a da kuma kulawa da mijinta, yan uwa da sauran Dangi duk baki daya don haka rayuwarta cike take da abin ko yi.
Da take gabatar da na ta jawabin Hajiya Tabawa, cewa ta yi kasancewarta da ta dade ta na yin harkar siyasa da Injiniya Dokta Kailani Muhammad ta san shi a matsayin jajirtaccen mutum da ke kokarin ganin talakawan kasa sun samu ci gaban da ya dace su samu ta yadda kasa za ta kai ga inda ake bukata.
Don haka samun mutane irin Injiniya Kailani Muhammad a cikin al’umma babbar nasara ce saboda irin kokarinsa da son ciyar da kowa gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Malam Imrana Abdullahi, da ya kasance ya san Injiniya Dokta Kailani Muhammad tsawon shekaru Goma sha Bakwai bayani ya yi a game da kokarin Injiniya Dokta Kailani Muhammad na son jama’a musamman talakawan Najeriya kasancewa sa wanda tun ya na yaro aka rika ba su tutar salama su na rikewa domin samun Akidar kishin kasa da son jama’a.
Ya kasance mai kokarin Sanya kansa a duk inda ake yin wani al’amari domin nemowa talakawan kasa yancinsu, wanda hakan ya dade ya na hidintawa tafiyar siyasar Muhammadu Buhari da dukiyarsa da kuma Karfinsa a koda yaushe tun da dadewa har Allah ya sa aka samu nasara a karkashin jam’iyyar APC.
Injiniya Dokta Kailani Muhammad ya zamo mutum mai kokarin fadakar da jama’a a kafafen yada labarai wanda dalilin hakan har sai da ya bude kamfanin wallafa jarida da ya Sanya wa su na “Librator” da ya bude mata ofishi inda ake gudanar da aikin tare da ma’aikata.
Ya kuma kasance mai kokarin fadakar da jama’a irin kokarin ayyukan raya kasa da wannan Gwamnatin take aiwatarwa domin jama’a hakan ya sa yake kiran taron manema labarai ya bayyanawa jama’ar da ya tara irin nasarorin da Gwamnatin Buhari ta samu a tsawon lokacin da ta kwashe a kan karagar mulkin Najeriya.
Kuma Injiniya Kailani Muhammad bai ta ba canza sheka ba irin yadda yan siyasa kan yi su rika tsalle daga wannan jam’iyya zuwa waccan daga nan zuwa can, shi bai ta ba yin hakan ba, ya kasance kaifi daya kawai shi ne a tafiyar Muhammadu Buhari a koda yaushe
Ya kuma zamo mai fadakar da jama’a a kafafen yada labarai na gida da na wajen Najeriya kamar irin su kafafen yada labarai na bbc,Muryar Amurka,radiyon Faransa da Muryar jamus, musamman abin da ya shafi siyasa da tattalin arzikin kasa da ya shafi harkar Man Fetur kasancewarsa masani a wannan fannin.
Taron dai ya samu halartar dimbin jama’a da suka hada da malaman addinin Islama da suka yi addu’o’in samun ci gaba da samun zuri’a mai albarka a game da wannan auren na Injiniya Dokta Kailani Muhammad da amaryarsa Khadija Bashir Mashi da a halin yanzu suka kwashe shekaru biyu har da samun da Namiji Muhammad Bashir Ishrak.

About andiya

Check Also

Ramadan 2023: Nigerian Church Reaches Out To Over 1000 Underprivileged Muslims/ Almajiri.

  The church of Christ Evangelical and life Intercessory Ministry, Sabon Tasha Kaduna State has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.