Home / KUNGIYOYI / Wanda ya gar gadeka, ya gama shiryaka: Damisa bata canza zanen jikinta.

Wanda ya gar gadeka, ya gama shiryaka: Damisa bata canza zanen jikinta.

 

Gaissuwa da fatan alkairi a gareku yan jarida.

 

 

Bayanai da suka iso ga kungiyar hadin kan matasan arewa shine kamfanin babbar matatar mai ta kasa a karkashin jagoran chin Mallam Mele Kolo kyari na shirye shiryen miqa contragin tsaron bututun matar mai zuwa ga makiyin qasa, dan fasa qwarin mai da fasa bututun mai da kuma sauran kayan aiki na gwamnati wai shi Oweizide Ekpemupolo wanda aka fi sani da Gwamnati Tompolo.

 

 

Wannan abin al’ajabi ne sosai, da hankali baze iya dauka ba ace a matsayin mu na qasa, zamu dauki tilon hanyar samun kudin qasar mu, mu danka amanar ta a hannun Tompolo, wanda ba a iya rabe sunan shi da fasa butun mai, satan mai, da barnar kayan gwamnati.

 

 

A matasyin mu na matasan arwar Nigeria, Tompolo daya yake da yan ta’adda kaman su Bello Turji, Nnamdi Kanu, Sunday Igboho, Muhammad Yusuf da sauransu, wa yanda basu daraja qasa, basu ganin komai illa watsewar Nigeria, rashin ladabi, da kuma rashin kunya ga Gwamnati me ci.

 

 

A matsayin mu na yan arewa wa yanda ke kula da gwamnati da harkokin gwamanti, a bisa yadda suka shafi yan qasa, baza mu tanqwashe hannuwan mu baa mu bari gwamnati tayi irin wannan gagarumin kuskuren danka bututun mata tar man mu a hannun wanda be dace ba, mara kishi qasa, mara tattali da adalci kuma makiyin ci gaban qasa.

 

 

Saboda haka, muna kira, muna roqo, muna kuma bada shawar ga kamfanin babban matatar mai na qasa cewa su temaki bututun ma’adanan mu na man petur kar su miqa kwangila tsoron su zuwa ga Tompolo saboda ze gur bata tattali arzikin Nigeria.

 

 

Idan aka bashi wannan kwangilar, sauran yan ta’adda kaman su Bello turji, da Nnamdi Kanuda zasu sa ran a basu kwangilar tsare fadar shugaban kasa, da iyalansa, da kuma shi kansa shugaban qasar.

 

 

Domin a nuna ma samari, manyan gobe cewa dogaro da kai, da neman na kai shi e yafi komai, ba shiga fituntunin zamani ba, da kuma sauran harkoki marasa kyau, kaman satar yanar gizo, da kingiyoyi na asirai dole ne a hana Tompolo wannan kwangilar, bama maganan bashi kwangila ba, dole ne a hana shi kusantar bututun mai na qasa baki daya.

 

 

Shawara kyauta ce, kuma ba a sayar da ita. Idan kunne ya ji gangar jiki ya tsira.

 

Abdulsalam Mohammed Kazeem

 

Maitaimakin Kaakakin Kungiyar matasan Arewa

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.