An haifi mai daraja Gwamna Abdul’Aziz Yari a ranar 28, ha watan Janairu, 1968. Ya kuma fara karatun makarantar Boko a makarantar Firamare ta Talatar Mafara, daga sai ya wuce makarantar horon malamai da ke garin Bakura da a yanzu haka ke cikin Jihar Zamfara daga shekarar 1979 zuwa 1984.
Ya kuma kammala karatunsu na gaba da makarantar sakandare a makarantar koyon ilimin kimiyya da fasaha (Polytechnic) da ke Sakkwato daga shekarar 1991 zuwa 1994.Inda ya samu takardar shedar kammala karatun satifiket kuma daga nan ya kammala karatun Difiloma a shekarar 2004. Ya kuma halarci makarantar ilimin kimiyya da fasaha ta Kebbi wato (Polytechnic) inda ya samu babbar Difiloma a fannin mulki a shekarar 2008.
Abdul’Aziz Yari, ya fara gudanar da harkokin siyasar shi ne tun daga shekarar 1999 da ya yi aiki a matsayin sakataren jam’iyyar ANPP na Jiha daga shekarar 1999 zuwa 2003. An kuma zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar ANPP na Jihar Zamfara a shekarar 2003 daga nan kuma likkafa ta yi gaba har ya zama sakataren kudi na kasa na jam’iyyar ANPP matsayin da ya rike har zuwa shekarar 2007 da aka zabe shi a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Anka da Talatar Mafara daga shekarar 2007 zuwa 2011.
A tsakanin, lokacin da Gwamnan Jihar Zamafara a wancan lokacin Mahmuda Aliyu Shinkafi, da ya koma jam’iyyar PDP mai mulki a wancan lokacin a wata Janairu 2009, sai kawai ya zama shi ne ya rungumi shugabannin jam’iyyar ANPP na Jiha duk suna tare da shi domin shike rike da su, har sai jam’iyyar ANPP daga hedikwatarta ta kasa da ke Abuja ya zama a dole aka samar da shugabannin rikon jam’iyyar karkashin Yari. Kuma a lokacin har sai da aka karawa wannan shugabannin riko lokacin gudanar da shugabanci duk a karkashin Yari sabida irin kokarinsa na shugabanci mai kyau.
A ranar 26 ga watan Afrilu, 2011, an zabi Abdul’Aziz Yari matsayin Gwamnan Jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar ANPP. Ya samu nasarar kayar da Gwamna mai ci a lokacin Gwamna Shinkafi da ya tsaya a jam’iyyar PDP a wancan lokacin.
Jam’iyyar ANPP na daya daga cikin jam’iyyun da suka hadu suka kafa jam’iyyar APC a halin yanzu a shekarar 2023.
Haka kuma a shekarar 2015 lokacin zaben Gwamna, an sake zabensa karkashin APC.
A ranar 18, ga watan Mayu, 2015, Gwamnoni abokan Honarabul Gwamna Yari, dukkansu suka amince da zaben sa matsayin shugabansu, inda ya ya maye gurbin Honarabul Chibuike Rotimi Amaechi.
Idan aka yi duba sosai a lokacin da ya na Gwamnan Jihar Zamafara a shekarar 2019, Yari ya tsaya zaben dan majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma kuma ya samu nasara da gagarumin rinjaye duk a karkashin jam’iyyar APC. Amma kuma sai kotun koli ta soke zabensa tare da na wasu yan jam’iyyar APC da suka tsayawa jam’iyyar takara a matakai daban daban bisa dogaro da cewa ba su gudanar da zaben fitar da ya takarar ba kamar yadda ya dace.
Kotun ta bayar da umarni ga hukumar zabe da ta Karbe satifiket din da ta ba su na shaidar sun lashe zabe kuma ta mikawa wadanda suka zo na biyu satifiket din lashe zabubbukan.Wanda haman ya bayar da dama ga jam’iyyar PDP ta amfana da darewa kan madafun iko sakamakon hukuncin kotun koli.
Kasancewarsa mutum mai yi wa jam’iyya biyayya ba da wasa ba, Yari ya ci gaba da zama a cikin jam’iyya tare da kare muradun ta duk da irin hukuncin da kotun koli ta yanke wa jam’iyyar APC a game da batun zabukan shekarar 2019. Duk da irin yadda al’amura suka gudana. Ya sake tsayawa takara domin zama Sanatan shiyyar Zamfara ta Yamma kuma ya samu gagarumar nasara a zaben da ya gudana a shekarar 2023, wannan ne ya sa a halin yanzu ya fito takarar neman zama shugaban majalisar Dattawa a majalisar karo na Goma (10), domin yin kyakkyawan shugabancin samar da dokokin da za su amfani kowa a ciki da wajen Najeriya baki daya.
Ba tare da wata tantama ba ko nuna alamun shakku Yari ya bayyana fili ya jagoranci samun nasarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa da ya gudana a wannan shekarar ta 2023 a Jihar Zamfara. Wanda ya tsayawa jam’iyyar takarar shugaban kasa kuma zababben shugaban kasa a yanzu Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,ya lashe zabensa ne a Jihohin Zamfara da Jigawa daga cikin Jihohin yankin Arewa maso Yamma a Najeriya.
Da ainihin irin kwarewar da yake da ita a fannin aikin majalisar tarayya idan aka hada da kuma dimbin ilimin da yake da shi na sanin harkokin siyasa yadda kabli da ba’adin ta yake da kuma sanin yadda ake jagorancin harkokin gudanar da mulki, tsawon shekaru Takwas da ya yi a matsayin Gwamnan Jihar Zamafara da kuma kasancewarsa Gwamna na farko da ya zama shugaban Gwamnonin Najeriya tsawon shekaru Hudu, Yari ya tabbata mutum wanda ya fi cancanta ya zama shugaban majalisar Dattawa ta Goma (10) da ta hada dukkan daukacin wakilan Najeriya guri daya, kuma matsayi na uku a kasa.