Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Aminu Ibrahim Goronyo ya bayyana cewa sakamakon irin yadda Gwarzon Gwamna Sanata Uba Sani ke aiwatar da ayyukan Ci gaban jama’a a dukkan fannonin Gwamnati yasa da kansa ya shiga zundum wajen fafutukar tallar ayyukan da Gwamnan ke aiwatarwa a Jihar Kaduna domin kowa ya fadaka cewa ya dace a sake ba Gwamnan dama karo na biyu domin ya maimaita wadansu shekaru hudu har a cika shekaru Takwas kamar yadda yake a Kundin tsarin Mulkin Najeriya.

Sama da kananan Asibitocin kula da lafiyar jama’a matakin farko da ake kira da, ( primary Health Centers) sama da 174 daga cikin 255 duk an daga darajar su zuwa matakai na biyu kuma ayyuka na ci gaba da sauran wadanda suka rage suma da nufin za a daga darajar su.
Dukkan wannan ayyukan da Gwamna Sanata Uba ke aiwatarwa ba wai kawai samar da wuraren ba ne kawai ko wadansu gine- gine ba ne kawai duk ana yi ne da nufin kare rayukan al’umma da kuma samar masu da karfin Gwiwa, tare da samar da tsarin kiwon lafiya mai inganci kusa da al’umma.

A halin yanzu a jihar Kaduna ana samawa jama’a wadanda suke a yankunan karkara cikin lunguna ingantattun magunguna ga al’ummar karkara, inda Mata ke samun biyan buƙatar kula da lafiyar su cikin sauki sakamakon irin yadda iyaye ke samu ana kula da lafiyar ƴaƴansu,wanda hakan ya sa iyalai ba sai sun yi tafiya mai nisa ba ko sun kashe kudi da yawa domin samun a kula da lafiyar su ba.

Hakika irin wannan aikin wata alama ce da ke nuni da irin kyakkyawan shugabancin da ake samu a Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Sanata Uba Sani da ke sauraren jama’a da biya masu bukatunsu don haka za a iya gane lallai idan aka samu jajirtaccen jagora irin Uba Sani za a iya samun kwalliya ta biya kudin sabulu a cimma nasarar da ake bukatar a samu.
Saboda haka muke bayyana cewa muna godiya da irin wannan jagoranci nagari da muka samu karkashin jagorancin Sanata Uba Sani domin irin yadda yake kula wa da batun samawa al’umma ingantattun abubuwan kula da lafiyar jama’a, hakika mun tabbatar da cewa kokarin Gwamna na taimakon dimbin miliyoyin jama’ar da ke a cikin jihar Kaduna.

Hakika Jihar Kaduna na bunƙasa, harkokin kula da lafiyar jama’a na bunƙasa, wanda sakamakon hakan ne shugaban tafiya Alhaji Aminu Ibrahim Goronyo ke cewa Gwamna Samata Uba Sani Sau biyu ne Insha Allah.
THESHIELD Garkuwa