Home / KUNGIYOYI / Wata Kungiya Ta Karrama Yusuf Danladi Da Lambar Yabo Ta Girmamawa

Wata Kungiya Ta Karrama Yusuf Danladi Da Lambar Yabo Ta Girmamawa

 

Ta ce Ya Cancanci Zama Shugaba A Kaduna Ta Kudu

 

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA Kungiyar mai suna yanzu ne lokacin kuma lokacin namu ne, “The time is now The Time Is Our (TIM) da ke garin Kaduna, ta karrama Yusuf Danladi mataimaki na musamman ga Tsohon Ministan Gona da aikace-aikace wato Honarabul Muhammad Mahmud, da lambar yabo ta girmamawa bisa irin gudunmuwar da ya bayar wajen ganin an gudanar da ayyukan raya kasa da al’umma a Jihar.

Yusuf Danladi wanda aka fi sani da Nadabo, kuma wanda ya kasance shugaban Matasa na Jam’iyyar APC ta Shiyyar ta biyu a Jihar Kaduna, ya Karbi shaidar lambar yabon ne a Karshen makaon nan a gidan sa da ke garin Kaduna.

Da yake jawabi jim kadan bayan karbar lambar yabon, Nadabo ya bayyana farin cikin sa bisa irin yadda ya’yan kungiyar suka ga cancantarsa a cikin sauran al’umma wanda har hakan yasa suka kai ga karrama shi da lambar yabo.

Acewar sa, wannan wani babban abin alfahari ne a gare ganin irin yadda al’umma suka yaba da salon Jagorancin shi a karkashin tsohon Ministan Gonan daya gudanar da wasu ayyuka na alheri ga al’umma domin cigaban su da kasa baki daya, wanda hakan ke nuna alamar cewa Gwamnatin su ta tabuka abun alheri a cikin al’umma.

Ya ce, “ina godiya sosai, saboda wannan kyautar ya nuna alamar cewa mutane na sane da irin ayyukan alherin da muke, kuma yin hakan zai sa nan gaba idan mun sake samun wata damar, za mu yi abin da yafi haka tun da su al’umma na yaba wa da nuna sanin ya kamata.

“Dama tun fil-azal, irin wannan aikin na al’umma shi muka gada domin iyayen mu sun koya mana tare da nuna mana sanin mahimmacin yiwa al’umma aiki, toh don haka zamu kara Jajircewa wajen ganin mun biyawa al’umma bukatun su a duk lokacin da muka samu wata dama a duk wata madafun iko.

“Ba shakka, wato ganin irin wadannan aikace-aikace da muke na al’umma ne yasa dayawa daga cikin al’umma suke ganin ya dace na fito takarar na tsaya Shugabancin Karamar Hukumar Kaduna ta kudu, toh kuma idan abin da al’umma suke so kenan, toh ba za mu watsa musu kasa a ido duk da har yanzu ban riga na amsa musu amma kuma muna kan shawarwari a game da wannan bukatar ta al’umma.” Inji Nadabo

Shi ma da yake gabatar da jawabin sa, shugaban Kungiyar Yunusa Muhammad, ya bayyana cewa a sakamakon ganin cancantarsa, kwazo da Jajircewa wajen rayu al’umma ne ya sanya Kungiyar ta ga ya zame mata wajibi ta karrama shi a matsayin wani gwarzo a cikin al’umma.

Ya ce, “Yusuf Danladi ya kasance wani abun alheri ga duk wani mai kishin kasa saboda kasancewar sa dan kasa nagari wanda ke kishin kasar sa da al’ummar ta domin baya nuna bangaranci a duk lokacin da aka saka shi a gaba wajen gudanar da ayyuka ga al’umma domin al’ummar ce kawai a gaban sa.”

Hakazalika, Jagoran tawagar Isma’il Mohammad Hari, ya bayyana taimaki ga Ministan a matsayin wazikin mutum wanda ya cancanci a yaba masa bisa irin gudunmuwar da ya bayar wajen kawo ci gaba a Jihar da kasa baki daya ta hanyar amfani da basirar sa yayin gudanar da duk wasu ayyuka.

Ya ce, “yanzu idan muka duba Karamar Hukumar Kaduna ta kudu da ta Arewa, Igabi, an samu canji na cigaba ta fuskar samar da hanyoyin kwalta a wurare daban-daban wanda hakan ya zama wajibi a yabawa kokarin da Honarabul Nadabo ya yi, domin hakan wata alama ce da ke nuni da cewa, idan har zai yarda ya tsaya takarar shugabancin Kujerar Ciyaman a Karamar Hukumar mu, toh al’umma zasu amfana da ribar romon dimokuradiyya a yankin.”

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.