Home / Big News / Wuta Ta Kama Babban Wurin Ajiyar Magungunan Jihar Kebbi

Wuta Ta Kama Babban Wurin Ajiyar Magungunan Jihar Kebbi

 Imrana Abdullahi
Sakamakon matsalar da aka samu na tashin Gobarar da ta tashi a Rumbun ajiye Magunguna na Jihar Kebbi inda magani na miliyoyin naira suka lalace.
 Wurin ajiyar magungunan da ya kama da wuta nan ne babban dakin ajiyar kayan kula da kiwon lafiya da suka hada da magani da sauran kayayyakin lafiya.
Gobarar dai ta kama ne har tsawon awa hudu inda ta cinye kayan kula da kiwon lafiya da Magunguna na miliyoyin naira tare da ginin baki daya.
Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu wanda aka gani yana kokarin kashe wutar da kansa tare da kwashe kayan da suka rage ya bayyana tashin Gobarar a matsayin wani mummunan hadari.
Ya ce ” a wannan yammaci akwai matsalar rashin Gobara a wurin ajiyar kayan kula da kiwon lafiya da Magunguna, amma dai an samu nasarar shawo kan lamarin tare da kokarin jami’an hukumar kashe Gobara na Jiha da jami’an tsaron filin Jirgin saman kasa da kasa na Sa Ahmadu Bello da kuma ma’aikatan lafiya na Jihar
 Duk wannan nankunshe ne a cikin wata takardar da mai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya Sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Gwamna Bagudu ya kuma yabawa dimbin jama’a masu fatan alkairi da shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati, Sakataren Gwamnatin Kebbi, Kwamandan jami’an tsaro na NSCDC, Kwamishinonin lafiya da ayyuka tare da Yan Sanda.
Sai kuma Daraktan Jami’an tsaron SSS, yan jarida bisa goyon bayan da suka bayar wajen kokarinnkwashe sauran kayan da suka tsira daga wutar.
 Duk da cewa har yanzu ba a san musababin tashin Gobarar ba Gwamnan ya bayyana lamarin da cewa wani lamari ne daga Allah domin haka ya kaddara

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.