Home / Big News / Abba Kyari Ya Rasu – Fadar shugaban kasa

Abba Kyari Ya Rasu – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasar tarayyar Nijeriya ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban ma’aikata a fadar marigayi Abba Kyari.

Kamar yadda bayanai suka fito daga ta hannun mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina, cewa fadar na matukar bakin cikin bayyana wa jama’a cewa Malam Abba Kyari ya rasu.

Marigayin dai an yi masa Gwajin cutar covid – 19 da ake Kira Korona bairus mai toshe Numfashi kuma tun daga lokacin yana ta amsar magani da kula game da cutar amma sai a ranar Juma’a, 17 ha watan Afrilu, 2020. Ya rasu inda ya koma ga mahalicci.

Kamar yadda sanarwar Femi adesina ta sanar cewa za a bayyana lokacin da za a yi masa Jana’iza nan gaba kadan.

Allah ya gafarta masa ya albarkaci abin da ya bari.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.