Home / MUKALA / YA AKE FULANI MAKIYAYA KE SAMAR DA NAMA A KASUWA KAN FARASHI MAI SAUKI ?

YA AKE FULANI MAKIYAYA KE SAMAR DA NAMA A KASUWA KAN FARASHI MAI SAUKI ?

 

 

 

Idan muka mayar da tsarin kiwon dabbobi na zamani, ya dace mu shirya samun sakamakon sa

 

 

– DAGA  GBENGA OLAWEPO-HASHIM

A matsayina na dan kasuwa kuma wanda yake da sha’awa kwarai a game da batun tattalin arzikin k’asa, koda yaushe na yi imanin cewa batun farashi alamace ta samar da kyakkyawan tsarin tattalin arzikin kasa da zai zamo zabi ga bangarori da dama.

 

 

A lokacin da ina makarantar sakandare, wasu daga cikin yan ajin mu su na kira na Baban masanin tattalin arziki “Baba Econs” , amma abin sha’awa, na rubuta jarabawar fita sakandare ta hukumar shirya jarabawa ta Afrika ta Yamma wato “WAEC” a matsayin mai rubuta jarabawa daga wajen makaranta. Lokacin ina dalibin ajin karamar sakandare, na rubuta jarabawa a kan darasin tattalin arziki, kuma hakika na yi farin ciki da sakamakon da na samu domin na samu sakamako mai daraja ta daya “A1”. Lokacin da na shiga jami’ar Buckingham a Ingila domin yin digiri na biyu, na yi godiya ga Allah na samu kyakkyawan sakamako mai darajar farko a darasin tattalin arziki na kasa da kasa da kuma harkokin kudi na kasa da kasa domin tabbatar da cewa irin karatun da aka yi a makarantar sakandare lallai ingantacce ne domin komai ya bayyana a fili ko a karatu a manyan makarantun jami’a na kasashen waje.

 

 

Don haka ya dace a dauki matakan samun sahihi kuma ingantaccen tsarin tattalin arzikin kasa, wanda a shirye nake a koda yaushe in ci gaba da bayar da gudunmawata a game da batun tattalin arzikin kasa.

 

 

Saboda haka, ni daya ne daga cikin ‘yan siyasa, da ba zai yuwu ba ace na san komai ba, don haka mu koma ga tambaya ta asali; wadanne abubuwa ne makiyaya wato masu kiwon dabbobi da suka bayar da gudunmawa har aka samu farashin nama mai sauk’i a duniya, wato ya zamo kilon nama daya ake samun sa a kan kudi dala $4.85, idan aka yi la’akari da irin yadda farashin nama ke da tsada a kasashen duniya, wanda a yanzu mafi yawan masu gabatar da bayanai da ke da tunani irin na mutanen kasashen Yamma ke kokarin mu koma a kan tsarin yadda ake yin kiwo a can kasashen waje; misali kamar a kasar Amurka, farashin Nama ya nunka a kalla da kashi biyar na irin farashin da ake sayar da kilon nama a Najeriya. Domin a Amurka kilon nama na kaiwa dala $24.18, a kasar Netherlands kuwa farashin kilon Nama na kaiwa dala $24.19 a kasar Israela kuwa farashin na kaiwa dala $21.49 a kan kowa ne kilon nama.

 

 

Na kuma sake bayar da lisafin farashin nama da ya shafi duniya.

 

 

Mene ne sakamakon zai kasance idan mun canza tsarin yadda muke samar da shanu da sauran dabbobin da muke samun nama daga gare su?

 

 

Na farko dai shi ne mu sani cewa makiyaya na daukar dabbobin su zuwa wuraren Kiwo inda ciyawa take, ba tare da biyan ko sisin kwabo ba.

 

 

Sai na biyu kuma shi ma ya yi kama da na farko domin makiyaya na daukar dabbobinsu zuwa mashaya ruwa, baya kawo wa dabbobinsa ruwan ta hanyar da take da wahala ta tsarin samar da ruwan noman rani da ke da bukatar sai an kashe kudi a cikin taarin biyan kudi na kasashen kuma ya zamo ana kulawa da tsarin ta hanyar wadansu kwararru daga kasashen waje.

 

 

Na uku kuma wanda shi ne mafi muhimmanci, mafi yawa shi ne tsarin samar da magani ko masana a kan harkokin bada magunguna, likitoci da dukkan masu duba lafiyar dabbobi duk a tsarin da ake bi a yanzu babu wannan, saboda a cikin daji kawai suke, kuma sun gaji tsarin ne tun daga iyaye da kakanni, amma a yanzu an rasa hakan. Kuma wannan ba zai zama irin yadda tsarin likitocon Dabbobi yake ba, amma zai taimaka masa ya samu sauki kwarai a batun maganar kiwon dabbobinsa.

 

 

Kuma shi ne ma’aikaci kuma mai kulawa da tsaron dabbobinsa kamar dai David a cikin littafin Baibul da ya saka rayuwarsa cikin hadari domin tseratar da Tunkiyarsa, da ya rika fada a fili da Zaki domin kare dabbarsa.

 

 

Mafi yawan mu a yau duk mun yi watsi da yin kokarin gabatar da ayyuka irin wannan wanda a can baya ya zaman wa masu yi al’ada da wasu za su iya yin gadon ta. Mu ce wasu mutane sun shirya wa shanu a rayuwarsa, batu na gaskiya shi ne duk wani batun sana’a da ake son ya samu ci gaba a rayuwa, dole ne sai an samu batun sha’awar yin hakan kafin ma ayi batun kudi. Mai yiwuwa shi ya sa makiyaya gujewa duk wani tsarin da zai jefa su a hannun ma’aikata masu yin aikin k’wadago da aka tsara za su kula da harkar kiwon dabbobi na zamani.

 

 

Ni ba Bafulatani ba ne, amma na girma ne a garin New Bussa cikin Jihar Neja da kuma Jihar Kwara, da ke kewaye da matsugunnin Fulani. Don haka ni ban girma da tunanin cewa za a iya ganin Fulani a matsayin masu matsawa sai sun bautar da wasu ba ko su karb’ewa wa’dansu mutane filaye ba, kamar  yadda a yanzu wadansu suke k’ok’arin bayyana lamarin ba, saboda tsananin talaucin wadansu yadda suke zaune a cikin mawuyacin hali ku san an san  haka ne lokacin da muka girma.

 

A batu na gaskiya, muna da yawa daga cikinsu a matsayin masu taimakawa, muna girmama su kuma muna koyi da abubuwa da dama daga cikin irin yadda suke da kuma sauk’in kansu.

 

 

Duk mun amince tsarin yin kiwon da ake k’ok’arin yin amfani da shi a halin yanzu da ake tunanin za a yi amfani da shi koda yake ana zuzuta batun ta hanyoyin da suke haifar da ru’du game da batun masu ta’addanci da sauran ayyukan batagari na makiyaya daga kasashen waje da suka kwararo cikin dazukan Najeriya, amma duk da irin yadda makiyaya ‘yan asalin k’asa suke gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya da jama’a kuma suke yin harkokinsu na kasuwanci tsawon lokaci.

 

 

Wasu daga cikin laifuka ko zunuban da ake ganin wadannan mutane na aikata wa sun hada da lalata filayen gonaki, fa’da da zaunannun manoma wanda a mafi yawan lokuta ke haifar da mutuwar mutane, shiga cikin filayen da ba na su ba kuma ba tare da izini ba, k’wace filaye, koda yake ba a san manufar al’ummar  Fulani ba ya zuwa yanzu.

 

K’warewar da nake da ita a game da batun tsarin tattalin arziki, na shaida mani cewa za mu iya barin tsari mai muhimmanci da muka sani kuma muka iya shi daga makiyayan mu na cikin gida da suka da’de su na tafiya a kansa – na Fulani makiyaya, mu fito da wata hanyar sabuwa daban na aiwatar da kiwon dabbobi.

 

 

Tsarin tattalin arziki na bangaren harkar noma ba zai zama wani batun son rai da siyasa ba, a’a ya zama ingantaccen tsarin tattalin arziki domin amfanin kowa. Batun yin kiwo irin na zamani da wasu Gwamnoni ke kokarin yi domin sun b’ullo da hakan zai samar da nama mai tsada fiye da yadda ake sayar da nama a kasar Amurka. Idan daga karshe aka tabbatar da shi, saboda samar da kayan da kuma yadda za a yi amfani da su zai sanya farashi ya yi tsada ta yadda mutane da dama ba za su iya ba.

 

 

A lokaci na karshe da na bincika,na duba farashin kwancen abin da za a yi amfani da shi mai akalla dubu 18,000 a kasar Argentina ya kai yawan kudi a lisafin dala $10M wato miliyan goma na dala, kwatankwacin naira biliyan biyar kenan na naira. Kuma ana bukatar irin wadannan kayan kiwon a kalla daruruwa da dama da kuma kudin kawo su Najeriya, da kudin cin hanci, kudin da za a biya na kasa zuwan su da wuri, na kunkoson da ke tashoshin Jiragen ruwa da dai sauransu.

 

 

Na fahimci cewa wasu mutane ba su damu da batun samun hauhawar farashi ba na tsadar Nama ‘ indai za mu farmaki Fulani.

 

 

Na tattauna da wani da ya mayar mini da amsa a cikin Yarbanci cewa ‘Aani tori pe a je,ka pe malu ni boda’ ma’ana dai shi ne (ba za mu wuce irin biyayyar da aka samar mana tin asali ba na girmama jama’a domin muna son yin amfani da nama ko cin nama ba). Hakan zai iya zama gaskiya ko kuma wata alama ce kawai ta nuna bambancin k’abila, amma dai tsarin kasa na noma kada a sake ya zama a kan batun son rai ko wani alamu na k’abilanci ,sai dai kawai a rik’a lisaafawa.

 

 

Hakika na karu da shawara a kan cewa, tsarin da zai kai ga makiyaya su kasance su na da iko a kan dabbobin su ba tare da shiga fili ko gonar wani ko wasu ba ,zai fi kyau kuma mafi inganci ta hanyar zab’i a kan tsarin da zai Jefa makiyaya a hannun wadansu ma’aikatan Gwamnati da ba su da wata kwarewar yin kiwon dabbobi a aikace kuma da ake ba su shawara daga wasu mutane a kasashen waje da ba  su san komai ba game da tsarin mu da yadda muhallin mu yake ba.

 

 

Tsarin Gwamnati na bunkasa wuraren kiwon dabbobi kada a sanya shi tilas ga duk  wata Jiha da ba ta bukatar yin sa, bayan hakan, dokar amfani da filaye a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na karkashin ikon Gwamnatin  jihohi ne. Don haka duk wadanda suke bukatar yin amfani da tsarin da zai haifar masu da tsada a kalla kashi biyar fiye da yadda lamarin yake a halin yanzu a bar su su aikata domin su na da yancin yin hakan, haka nan kuma duk wadanda suke bukatar yin amfani da tsari mai sauki su ma su na da yancin yin hakan, kuma wannan shi ne tsarin tarayya na gaskiya.

 

 

Kalmar da ya dace a kiyaye da ita musamman ga jami’an  Gwamnatin tarayya. Duk yadda matsayarsu ta kasance, dole su ko yi yadda ake aiwatar da lamarin sadarwa ko samun bayanai. Kada su yi sakacin cewa Fulani makiyaya wadansu irin mutane ne na daban don haka a mayar da su wata al’umma mai hadari.

 

Dukkan manoma da makiyaya ‘yan Najeriya ne, don haka k’ok’arin mu na bunkasa duk abin da muka sani game da lamarin a harkar noma, sai a zamanantar da abin, da nufin k’ara masa inganci, amma ba mu rushe shi baki daya ba, saboda ingantawa da zamanantar da tsarin zai ba mu damar samun zaman lafiya da tsaro.

 

 

Ina sane cewa wannan matsaya da na dauka zai iya kawo ka ce- na ce, amma duk wanda yake da wani tsarin da za a iya amfani da shi, hakika ya dace ya hanzarta bijirowa da tsarin domin a tattauna a kansa da nufin a samu ingantacciyar sahihiyar matsayar da za ta amfani kasa baki daya.

 

 

Gbenga Olawepo-Hashim, ‘dan kasuwa,’dan siyasa ne wanda ya tsaya takaran shugaban k’asa a 2019.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.