Home / News / Gwamna Zulum Na Aikin Ciyar Da Jihar Borno Gaba – Bukar Dalori

Gwamna Zulum Na Aikin Ciyar Da Jihar Borno Gaba – Bukar Dalori

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Sakamakon aiki tukuru a kowa ne lokaci domin ciyar da Jihar Borno gaba ya sa al’ummar duniya ke yin jinjina da Yabo ga Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum.

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa reshen Jihar Borno Alhaji Ali Bukar Dalori ya bayyana Gwamna Zulum a matsayin mai gaskiya da rikon Amana tare da kishin jama’ar Nijeriya.

 

Alhaji Ali Bukar Dalori ya ce Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum, a matsayin shugaban da ke da nagartar da babu wata tantama a kai da yake kokarin habbaka daukacin al’amuran Jihar Borno baki daya.

 

Shugaban na APC Bukar Dalori ya bayyana hakan ne lokacin da tattauna da manema labarai ta wayar hannu a garin Kaduna.

 

Ya kara jaddada Gwamna Zulum a matsayin mutum mai mai kokari tare da kishin jama’ar kasa da ya sadaukar da kansa domin kasa ta ci gaba.

 

Alhaji Ali Dalori ya kuma yaba wa Gwamnan bisa irin kokarinsa da dagewa har ya samar da dimbin ayyukan da suka kai guda dari biyar da Hamsin da shida a cikin shekaru biyu.

 

Shugaban wanda ya kasance shi ne shugaban kungiyar shugabannin jam’iyyar APC na kasa ya fayyace kokarin Gwamna Zulum da cewa lamari ne da a fili ya tabbatar da bunkasa Jihar Borno baki daya.

 

Sai ya ci gaba da bayyana gamsuwarsa da irin ayyukan ciyar da bangarorin Ilimi,lafiya da aikin Gona gaba da sauran bangarorin ciyar da tattalin arzikin kasa gaba tare da sauran fannoni da suka hada da samar da aikin yi, walwalar jama’a da magance matsalar fatara da talauci da samar da abinci da abubuwan more rayuwa da suka hada da yan gudun hijira.

 

Alhaji Ali Bukar Dalori kira ya yi ga daukacin sauran jihohi da su yi ko yi da abin da Gwamna Zulum ke aiwatarwa a Jihar Borno wanda ya zama daban da abubuwan da suka faru a tarihin Jihar tun farko.

 

 

Shugaban na APC ya ci gaba da bayanin cewa sakamakon aikin da Gwamna Zulum ke yi za a rubuta sunansa da ruwan zinare sakamakon yadda yake aiwatar da shugabancin Jihar bisa tabbatar da gaskiya da adalci.

 

“Tun da Gwamna Zulum ya dare kan karagar mulkin Jihar Jihar aiwatar da muhimman gyare gyare a bangarorin tafiyar da aikin Gwamnatin jihar”.

 

A game da batun harkokin tsaro, Alhaji Ali Dalori suk da irin yadda wasu ke kokarin haifar da matsala a Jjhar Gwamna Zulum ya samu nasarar ci gaba da shugabanci a Jihar kamar yadda ya dace.

 

Ya kuma bayyana gamsuwa da Yabo ga tsohon Gwamnan jihar Sanata Bukar Kashim Shatima, da ya kawo Farfesa Babagana Umara Zulum ya zama Gwamnan Jihar Borno da a halin yanzu aka samu ci gaban da kowa ke murna da hakan

 

 

Shugaban jam’iyyar ya kuma yi kira ga daukacin jama’a da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamna Zulum a kowa ne fanni domin ciyar da Jihar gaba.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.