Home / News / Ya Dace Gwamnati Ta Samar Da Mafita – Felix Hyate

Ya Dace Gwamnati Ta Samar Da Mafita – Felix Hyate

Ya Dace Gwamnati Ta Samar Da Mafita – Felix Hyate
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna Honarabul Felix Hassan Hyate, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’, da ta samar da wata mafita ko wani ingantaccen tsarin da zai kawo sauki ga dukkan mutanen da aka sace suka shiga hannun yan bindiga.
Felix Hassan Hyate ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ankarar da Gwamnati cewa idan ta ce ba za ta tattauna da yan bindiga ba  kuma ba za ta bayar da kudin fansa ba to, ya dace ita Gwamnati da kanta ta samar da wata hanyar da za ta zama mafita ga halin da ake ciki musamman domin wadanda ke hannun yan bindiga su samu sauki tare da kubuta daga hannun mutanen da ba su da tabbas.
“Samar da mafita ga dukkan wanda ke hannun yan bindiga abu ne mai matukar muhimmanci saboda su ba wani abin da ke gabansu suke da bukata kamar kubuta daga hannun yan bindigar da suke Garkuwa da su saboda haka ya dace Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da wani ingantaccen tsarin da zai haifar da mafita”.
Ya ci gaba da cewa “akwai wata mata da mijinta ya mutu kuma ga yayanta sun samu makaranta za a biya masu kudin makaranta, amma an yi wa gidanta lamba za a rushe gidan, ka ga a halin da wannan matar take ciki Allah kadai ya san irin yadda yanayinta zai kasance da abin da zai iya faruwa, saboda haka lamarin abin dubawa ne kwarai”.
Muna kiran al’ummar Jihar Kaduna da su bude idanunsu a lokacin zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli mai zuwa su bayar da hadin kai da goyon baya ga hanyar zuba kuri’unsu a inda ya dace jam’iyyar PDP da yan takararta su samu shiga dukkan madafun ikon karamar hukuma guda 23 na Jihar Kaduna baki daya”.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.