Home / News / Zan Inganta Rayuwar Mata Da Matasa – Zailani

Zan Inganta Rayuwar Mata Da Matasa – Zailani

Imrana Abdullahi
Zailani A J Musa dan takarar shugaban karamar hukumar Kaduna ta Kudu da ke neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takara ya shaidawa manema labarai cewa zai mayar da himma wajen taimakawa mata da matasa domin ciyar da al’umma gaba.
Zailani A J Musa wanda ya kasance matashi ne ya yi tilawar irin yadda yake kokarin bunkasa rayuwar a duk fadin karamar hukumar ba tare da nuna wani bambanci ba a tsakanin jama a ba.
“Mun taimakawa rayuwar jama’a da dama ta fuskar Koyar da su sana’o’i kala daban daban da nufin kowa ya samu ingantacciyar rayuwa, kuma mun yi hakan ne a tsawon lokacin shekaru da dama wannan mutane da yawa sun hakan don haka mu duk harkarmu ta jama’a ce a koda yaushe”.
Ya ci gaba da cewa zai yi jagorancin Gwamnati ne a bude da za a rika yi da kowa da kowa a gwamnatance kowa ya san ana yi da shi.
Zailani A J Musa, ya kuma yaba da irin yadda jam’iyyar PDP ta gudanar da aikin tantance yan takarar da za su tsaya mata zaben shugabancin kananan hukumomi inda ya yaba kwarai da yadda lamarin ya gudana kasancewarsa daya daga cikin wadanda aka tantance a ofishin jam’iyyar na Jiha.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.