…tattalin arziki na samun ci gaba kwarai
Daga Imrana Abdullahi
An bayyana tattalin arzikin Najeriya a matsayin wanda ke samun gagarumin ci gaban karuwa da karbuwa a tsakanin al’ummar duniya baki daya.
Farfesa Kailani Muhammad ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Abuja.
Farfesa Kailani Muhammad ya tabbatar wa da duniya cewa Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na iya kokarin ta wajen ganin tattalin arzikin ya ci gaba da inganta a koda yaushe.
Sabanin irin yadda wadansu mutane ke kokarin mayar da batun tattalin barzikin Lamar wani abu da ban.
Farfesa Kailani Muhammad ya ci gaba da yin kira ga wadansu Jagororin kasar nan da suka hada da Atiku Abubakar da Peter Obi da su rika yin magana suna tattauna duk wani batu kafin su furta wata kalma, musamman ta yadda za su iya bayar da shawarwari ta hanyoyin da duka dace ga shugaban kasa ta ingantattun hanyoyin da suka dace wanda dukkansu sun san hanyoyin da niyyar kasa ta ci gaba a wannan yanayin.
Hakazalika Farfesa Kailani, ya kuma yi kira ga shugabanni da yayan kungiyar kwadago ta kasa da suma su rika tattauna batutuwan da za su dace bisa la’akari da halin da tattalin arzikin kasa yake ciki, ta yadda za a samu matsaya a kan batun karancin Albashi.
Saboda haka ne muke yin kira ga yannkwadago da cewa su daina mancewa fa akwai wadansu Jihohin da har yanzu ba su iya biyan karancin albashin ma’aikata na kashi Talatin cikin dari balantana a rika batun Albashi na makudan kudi masu yawa a ina za su samo kudin?
Hadaddiyar kungiyar da ta hada kungiyoyi karkashin jam’iyyar APC sun kuma yaba wa Jami’an yan Sandan Najeriya a bisa kokarinsu da suke ba dare ba rana domin ganin an yi maganin batagari a duk inda suke a cikin kasa