Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
A kokarin ganin rayuwar matasa ta ci gaba da inganta a duk fadin karamar hukumar Funtuwa da Jihar Katsina baki daya ya sa aka shirya wani babban taron fadakar da matasa da kuma sauran jama’a.
An dai yi babban taron ne a babban dakin taro na kwalejin horar da ma’aikatan Gwamnati domin sanin dabarun mulki da dukkan tsarin shigabanci da ake kira “College of administration”, da ke da matsugunni a Unguwar Magajin Makera karamar hukumar Funtuwa cikin Jihar Katsina.
An dai gabatar da kasidu da jawaban fadakarwa da Jan hankulan matasa musamman masu ta’ammali da shan kwayoyin gusar da hankali da kuma aikata wadansu ayyukan badala a cikin al’umma.
Tun da farko farfesa Usman Zunnuraini daga jami’ar Bayero Kano ya gabatar da mihimiyar kasida mai cike da Jan hankali da fadakarwa da yakamata a san yadda ma za a nemi aure kasancewar muhimman matsalolin da matasa ke fuskanta wani al’amari ne da ke farawa tun daga gidan iyayen da suka haife su, sai kuma matsalar rashin ilimi inda ya ce ba yadda za a yi mara ilimi ta iya bayar da ingantacviyar tarbiyyar da ta dace.
A dai wajen taron malaman kungiyoyin addinin musulunci na kungiyar Izala da Darika duk sun gabatar da jawabai da fadakarwa ta fuskar addinin Islama da taarin zamantakewa.
Malam Abdurrahman Funtuwa ya fadakar tare da Jan hankulan masu hannu da shuni da kuma mawadatan da suke a cikin al’umma da su rika duba jama’ar su wajen samar da Kamfanoni da dukkan abubuwan da za su ciyar da rayuwar bil’adama gaba sai kuma a rika taimakawa matasa kamar yadda ya bayyana a wirin jawabinsa a taron.
Shima Liman Abubakar Liman Sa’idu Funtuwa, kira ya yi ga matasan da su hanzarta kula da rayuwarsu kasancrwar hanyar da suka dauka ta shaye shaye cike take da dimbin matsaloli masu hadarin da za su iya taimakawa matashi ya rasa ransa a cikin kankanin lokaci.
Sai ya yi kira gare su matasan da su hanzarta dawowa cikin hayyacinsu ta yadda za su bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban kasa da jama’arta baki daya.
A wajen taron an gabatar da jawabai da dama inda har su ma matasan suka gabatar da jawabai da kuma yin namijin kokarin gabatar da kwayoyi da sauran kayan mayen da suke dauke da su a wajen taron, wanda hakan alamace ta tuba da ke alamta cewa sun tuba sun daina aikata shaye shaye da ayyukan assha da suke aikatawa a can baya.
Sarkin Matasan Funtuwa ya bayyana irin yadda suka sha fama wajen ganin matasan nan sun fahimce su har ma su ba su hadin kan amsa tambayoyi da kuma yi masu bayanin abin da ya dace game da harkar shaye shaye da sauran ayyukan Assha da suke aikatawa.
” har cewa suka yi za a sa ne jami’an taaro su kamasu muka ce masu ba haka ba ne, mun dai kwashe tsawon watanni muna kokarin shawo kan matasan nan domin su fahimci abin da muke so da yadda za mu yi da su, har sai da muka samu nasarar shawo kansu”, Inji Sarkin Matasa.
An dai gudanar da taron ne tare da dukkan irin wadannan matasan da ke bukatar su zama mutanen kirki a cikin al’umma.
Taron dai ya samu halartar mai girma Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtuwa, Alhaji Sambo Idris Sambo da kuma Magajin Funtuwa da kuma Magajin Makera da aka yi taron a yankinsa.
Ya kuma samu halartar muhimman mutane da dama a ciki da wajen karamar hukumar Funtuwa.
An kuma karrama wadansu fitattun mutane da lambskin yabo domin nuna jin dadi da karramawa a game da irin abubuwan da suka yi na Ci gaban rayuwar jam’a baki daya
THESHIELD Garkuwa