Dubban jama’a ne suka mamaye manyan ƙauyuka da hanyoyin da ke kaiwa garin Ɗansadau domin tarbar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a wata ziyara ta tarihi da ya kai yankin.
A ranar Laraba ne gwamnan ya ziyarci al’ummar Ɗansadau da ke Ƙaramar Hukumar Maru, ziyara da ta ɗauki hankalin jama’a tare da nuna farin cikin al’umma bisa zuwansa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa kusan shekaru fiye da ashirin kenan rabon da wani gwamnan Zamfara ya taka ƙafa zuwa Dansadau, tun daga zamanin tsohon gwamna Ahmad Sani Yariman Bakura.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Dansadau, wadda ita ce mafi girman gunduma a Ƙaramar Hukumar Maru, ta shafe tsawon lokaci cikin mantuwa da sakaci daga gwamnatocin baya, duk da girman al’ummarta da muhimmancinta ga ci gaban yankin.
A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya ratsa wasu al’ummomi da suka haɗa da Wanke, Magami da Dan Gulbi, inda jama’a suka fito kwansu da kwarkwata domin nuna masa ƙauna da goyon baya.
Gwamnan ya kuma duba aikin gina titin Gusau zuwa Dansadau mai tsawon kilomita 108, wanda gwamnatinsa ta bayar da kwangilar aiwatarwa a matsayin wani muhimmin bangare na ƙoƙarin buɗe hanyoyin sufuri da bunƙasa tattalin arzikin yankin.
A wani bangare na ziyarar, Sarkin Dansadau, Mai Martaba Alhaji Garba Mohammed Sarkin Kudu, ya karrama Gwamna Lawal da sarautar gargajiya ta Garkuwan Dansadau, a matsayin girmamawa ga yadda ya nuna damuwa da sha’awar kawo ci gaba ga yankin.
Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa wannan ziyara ta nuna ƙarara ƙudurin Gwamna Lawal na sauka ƙasa-ƙasa domin kusantar al’umma da kuma tabbatar da cewa ayyukan raya ƙasa sun shafi dukkan sassan jihar. Tarbar da jama’ar Dansadau suka yi masa na nuni da ƙaruwar goyon bayan da gwamnatinsa ke samu, sakamakon manyan shirye-shiryen raya ƙasa da ake aiwatarwa ƙarƙashin manufar ‘Zamfara Rescue Mission’.
A cewar jama’a, ziyarar gwamnan ta sake farfaɗo da fata da kwarin gwiwa cewa Dansadau da makamantanta ba za su sake zama a bayan layi ba a tsarin ci gaban jihar Zamfara.
THESHIELD Garkuwa