Home / Labarai / YAKAMATA YAN NAJERIYA SU YI KISHI DA ZUCIYA WAJEN SARRAFA AMFANIN GONA – IDRIS MIKATI

YAKAMATA YAN NAJERIYA SU YI KISHI DA ZUCIYA WAJEN SARRAFA AMFANIN GONA – IDRIS MIKATI

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Alhaji Shu’aibu Idris Mikati, shugaba ne da ke kokarin Tallafawa rayuwar al’umma ya bayyana samun kishi, jajircewa tare da tsoron Allah a matsayin abin da zai tabbatar da sahihin gyara a Najeriya.

Shu’aibu Idris Mikati ya kuma yi kira ga daukacin al’umma da su dauki halin nuna kyama da duk wani dan abin hannun da ba a san inda mutum ya samo shi ba zai rika ba jama’a, domin in ba haka ba gyaran Najeriya sai dai daga Allah madaukakin Sarki.

Mikati ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.

Ya ci gaba da bayanin cewa ” ban da Man fetur muna da ma’adinai kala – kala kamar Zinari, Tagulla, Azurfa ga kuma hasken rana, Ruwan Sama a lokaci lokaci ga kuma kasar Noma kuma Allah ya albarkaci kasar nan da jama’a Sama da miliyan dari biyu ga kuma mutane masu basira wanda kasidu bisa kasidun da masana suka rubuta babu iyaka domin yawan su koda za a cika Daki ko Falo ba za a samu wurin ajiye su ba.

” Ba sai an he wani nesa ba ya dace a koma Noma kawai, mu tabbatar da muna iya ciyar da kan mu kuma ya dace a taimaka wajen kiwon lafiya mu tabbatar da cewa kananan cututtuka ba sai mutum ya tashi ya ta fi kasashen Ketare ba domin ya samo magani ba domin yakamata ma’adinai da Allah ya albarkace mu da su an hakosu ana amfani da su don a samu kudin shiga wadannan ne za a samu domin a fadada kudin shiga a inganta tattalin arzikin kasa”.

Kuma “Albarkatun Gona da muke da su kamar Ridi, Yazawa, Tabo wato Kadanya da Citta a tabbatar da cewa an jawo hankalin masu hannu da shuni suyi masana’antun da za a sarrafa su a nan gida Najeriya domin yayan mu in sun kammala makaranta su samu inda za su makale su fara rayuwarsu, ko ba su taimaki kowa na su taimakawa kansu da kansu.

Sai kuma a game da batun yin amfani da yanar Gizo da wasu batagari keyi domin yin zamba cikin Aminci ko sata kai tsaye kuwa, sai Mikati ya ce batun sata da ake yi a yanar Gizo ya shafi mutane da dama domin ni kaina ya shafe ni, domin an taba yi Mani wannan kuma na yi asarar kudi masu yawa sai dai ba a taruwa a zama daya wasu na da imani wasu kuma na da karancin imani wasu nada tausayi wasu ba su da tausayi saboda haka dole kusan koda yaushe mu zauna muna dar – dar domin akwai barayi masu sata da  bindiga da masu shiga su yi wa jama’a sata  akwai kuma masu tare mutane ko Karbe masu wayoyi daban daban dai ga su nan saboda haka abin da zamu yi shi ne kawai addu’a domin neman kariya daga Ubangiji Allah ga bawan ka ko ga bayinka Allah ka taimake mu ka kare mu daga sharrin abin halitta kowace iri ce domin ba wani magani da ya wuce addu’a kuma ka zauna cikin shiri don duk abin da ka san babu gaskiya a ciki ka guje shi.

Sai maganar ace wasu sun taso daga wadansu kasashe su sarrafa kayan Gonar mu, to, idan mu da muke a kasar bamu yi amfani da arzikin ba sai wani ya taso daga wani wuri can daga wata kasa ya yi amfani da arzikin namu ya sarrafa to, ai duniya ta zama a gari daya.

” Yayan jama’ar Indiya da Caina a yanzu sune ke juya tattalin arzikin kasar Najeriya , Kamfanin da ya fi kowa cinikayyar ridi da Citta da Kashu ba kamfanin yan Najeriya bane, na wasu yan Indiyawa ne. Kaga mu muna da masu hannu da shuni amma ba su yi ba tun da ba su yi ba arziki na Allah ne ya ba mu kuma bakin suna da Gonakin ne ba su da su duk yan Najeriya ne keda su kuma a wurinsu suke sayen kayan nan. Yanzu idan kaje garin Kano ko Sakkwato zaka ga cewa suwa ne ne suka fi sarrafa fata ta Dabbobin da yake yanka wa sai kaga mutanen Kwarori ne yan kasar Labanan da sauran yan siriya da suke cinikayyar, tun da mu da aka san mu da Jimar fata da Rini Bama yi sai wasu da suka taso daga kasashen Ketare sun zo sun kuma yi ai wata kila dai muma mu tashi tsaye mu yi zuciya muce bari mu tashi tsaye mu kamanta abin da suke yi domin su ba wasu halitta bane da suka sha bamban da irin namu halittar ba don haka yakamata mutu zuciya mu kuma yi kishi da hobbasa wajen raya wannan kasar da tattalin arzikin ta baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.