Home / Ilimi / Yan bindiga Sun Harbe Daliban Jami’a Uku Da Suka Sace

Yan bindiga Sun Harbe Daliban Jami’a Uku Da Suka Sace

Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Gwamnatin Jihar Kaduna na cewa yan bindigar da suka sace daliban jami’ar  Greenfield mai zaman kanta da ke Kaduna sun halaka guda uku daga cikinsu.
Kamar yadda wata sanarwar da ke dauke da sa hannun Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar kaduna Malam Samuel Aruwan ya Sanya wa hannu aka rabawa manema labarai ta tabbatar da cewa an tsinci Gawar daliban guda uku a mace.
A wani tsarin da ke nuni a fili cewa akwai matsalar rashin hankali tattare da rashin tausayi a irin yadda yan bindigar suka kashe daliban da suka sace a cikin jami’ar Greenfield tsawon milimita 34  Kan titin Kaduna zuwa Abuja.
A ranar Talata ne da ta gabata da dare wadansu yan bindigar da ba a gane yawan su zuwa yanzu ba suka kutsa kai cikin jami’ar da ke Kauyen Kasarami cikin karamar hukumar Chikun.
An dai tsinci Gawar daliban ne a yau Juma’a a kauyen Kwanar Bature wani kauye ne kusa da jami’ar, kuma Kwamishinan harkokin cikin gida na Jihar Kaduna da kwamandan thunder strike, Laftanar Kanar MH Abdullahi sun kwashe gawarwakin zuwa wurin ajiye gawa na asibiti.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmad El- Rufa’I tuni ya yi Allah wadai da wannan kisan da ya bayyana da rashin hankali inda ya ce hakika wadannan yan bindiga sun bayyana tsananin rashin Imani ga rayuwar dan Adam don haka dole ne a yake su kamar yadda suka bukaci yin hakan.
Gwamnatin ta yi bayanin cewa za ta ci gaba da bayar da bayanin abin da yake faruwa game da lamarin.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.