Home / Labarai / Yan bindiga sun sace amarya a Katsina

Yan bindiga sun sace amarya a Katsina

Yan bindiga sun sace amarya a Katsina

Wasu ‘yan bindiga sun shiga garin Kafin Soli, karamar hukumar Kankiya jihar Katsina, suka sace amaryar wani mutum mai suna Ahmad Muhammad.

Mazauna yankin sun fada wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun shiga garin ne da misalin karfe 12 na yau Laraba, inda suka kwashe kusan awanni 3 kafin nan su sace amaryar su tsere da ita bisa babura.

Jaridar Katsina Beat ta rawaito cewa mazauna yankin sun yi hasashen cewa ‘yan bindigar sun je harin ramuwar gayya ne kan wadansu masu bayanan sirri 5 da jami’an tsaro suka kama a kwanakin baya.

Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta hannun mai magana da yawunta Gambo Isah ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta na bakin kokari domin ganin sun ceto matar, tare da kama wadanda suka yi aika-aikar.

About andiya

Check Also

With Buhari’s directive, Zulum moves to re-open farms along Mulai-Dalwa axis 

  Borno State Governor, Babagana Umara Zulum on Sunday visited Mulai and Dalwa communities and …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *