Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Zamfara na cewa wadansu yan bindiga sun sace daliban makarantar koyon aikin Noma da ke garin Bakura.
Kamar yadda rahotannin suka bayyana cewa dalibai Goma sha biyar (15) ne yan bindigar suka sace.
Sai dai a wata majiyar da ba mu tabbatar da sahihancin bayanin ba na cewa wadansu mutane da suka hada da yan gadi sun rasa rayukansu.
Za mi ci gaba da kawo maku yadda labarin yake kasancewa…