Home / News / Injiniya Nura Khalil Ya Dawo Jam’iyyar APC

Injiniya Nura Khalil Ya Dawo Jam’iyyar APC

Mustapha Imrana Abdullahi
Fitaccen dan siyasa da ya dade ya na Gwagwarmayar neman kujerar Gwamnan Jihar Katsina Injiya Muhammad Nura Khalil, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar APC domin ya ci gaba da taimakawa shugaba Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari.
Ya tabbatar da hakan ne inda ya ce ya yanke wannan shawara ne ganin cewa daman babu wanda ya kai shi yin Hobbasa a ciki jam’iyyar ANPP karkashin jagorancin Muhammadu Buhari da kuma Jam’iyyar CPC  can baya.
Ya ce daman can Muhammadu Buhari ba siyasa ce ta hada su ba aiki ne da mu’amalla ta mutunci da martaba Juna.
Kuma ya kara da cewa ” a halin yanzu kusan dukkan magoya bayansa da suke harkokin siyasa tare su na cikin jam’iyyar APC don haka ya yanke wannan shawara ta shiga cikin siyasar gadan gadan kamar yadda yake yi a shekarun baya da suka gabata saboda jama’a da dama sun same shi sun kuma gaya masa a matsayin shawara cewa ya dace ya koma jam’iyyar APC domin nan ce ta fi dacewa da shi,” inji Nura Khalil.
Sabida haka na yanke shawarar dawowa cikin jam’iyyar APC duk da cewa ni ina da sana’a kuma ina da abin yi na kashin kaina har ina taimakawa wadansu ta hanyar daukar aiki domin su kula da iyalansu da dukkan abokan arziki.
“Ni dan karamar hukumar Bakori ne cikin Jihar Katsina amma saboda yanayin aiki na yi makarantar Firamare a wurare da dama da suka hada da Firamare ta Nadabo Bakori, Gidado,Kachiya da sauran wurare har na kammala na kuma yi makarantar sakandare ta Barewa kuma na yi digiri a fannin Injiniya gine gine, na fara aiki a kamfanin gine gine na Barade a Sakkwato daga baya na kafa nawa kamfanin

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.